Adamawa: “Ku Gaggauta Dawo Da Tattara Sakamakon Zabe, Atiku Ga INEC

Adamawa: “Ku Gaggauta Dawo Da Tattara Sakamakon Zabe, Atiku Ga INEC

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya magantu a kan cikon zaben gwamnan jihar Adamawa
  • Atiku ya bukaci hukumar zabe ta kasa da ta gaggauta dawo da shirin tattara sakamakon zaben da ya gudana a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu
  • Ya zargi hukumar zaben da shirin yin murdiya ga muradin al'ummar jihar Adamawa yana cewa INEC ta daura damarar ayyana APC a matsayin wacce ta lashe zabe a kowani hali

Adamawa - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bukaci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta gaggauta dawowa bakin tattara sakamakon zaben gwamnan Adamawa.

Hukumar INEC ta dakatar da tsarin bayan baturen zabe na jihar ya ayyana yar takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben.

Kara karanta wannan

Fintiri vs Binani: Gwamnan Adamawa ya yi bayani game da kitimurmurar zaben jihar

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Paul Ibe ya fitar, Atiku ya ja hankalin yan Najeriya zuwa ga "shiri na kokarin juya muradin mutanen jihar Adamawa a zaben gwamna a jihar', jaridar Daily Trust ta rahoto.

Shugaban hukumar zabe na kasa
Adamawa: “Ku Gaggauta Dawo Da Tattara Sakamakon Zabe, Atiku Ga INEC Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

Atiku ya ce matakin farko da baturen zaben jihar Adamawa ya dauka na ayyana yar takarar APC, Sanata Aisha Binani, a matsayin wacce ta lashe zaben wani lamari ne da ke nuni ga yanayin zaben 2023 gaba daya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar ta nakalto wani bangare na sanarwar yana cewa:

"A Adamawa, muna fuskantar kwaikwayon labari a a gudanarwar zabe inda kwamishinan zabe ya sanar da wacce ta fadi a zabe a matsayin wacce ta yi nasara.
"Shakka babu cewa INEC ta tunkari zaben jihar Adamawa da ajandar ayyana APC duk ritsi duk wuya.

Kara karanta wannan

Adamawa: Hukumar INEC Ta Kasa Ta Yi Karin Haske Kan Ayyana Binani a Matsayin Sabuwar Gwamna

"Saboda haka a kan wannan ne muke jan hankalin duniya zuwa ga shirin da INEC ke yi na murde muradin mutanen jihar Adamawa.
"Muna kuma son sanar da duniya cewa irin wannan dabi'a na INEC na illa na hargitsa zaman lafiya da tsaron al'umma.
"Mun ga yadda INEC ta gudanar da zabukan ranar 25 ga watan Fabrairu da na 18 ga watan Maris ba yadda ya dace ba sannan ta kalubalanci yan takarar da aka cuta da su garzaya kotu, ganin cewa sun san me suka taka."

Ya kamata a kama duk masu hannu a shirin cin amanar mutanen Adamawa, Atiku

Atiku ya kuma yi kira ga kama baturen zaben Adamawa da sauran mutanen da ke da hannu a wannan aiki na cin amanar kasa ba tare da bata lokaci ba sannan a hukunta su daidai da doka.

Wasu mutane sun tube kwamishinan zabe na kasa a Adamawa

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun yi wa wani kwamishinan zabe na kasa zigidir a jihar Adamawa yayin cikon zaben gwamnan 2023 a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng