Adamawa: INEC Ta Nesanta Kanta Daga Sanar Da Samun Nasarar Binani, Ta Dakatar Da Tattara Sakamako
- Hukumar zaɓe INEC ta soke sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa wanda REC ya baiwa Sanata Binani nasara ranar Lahadi
- A wata sabuwar sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta, ta sanar da dakatar da tattara sakamakon
- A dazu, shugaban INEC reshen jihar Adamawa ya ayyana Yar takarar APC a matsayin wacce ta samu nasara a zaɓen Asabar
Hukumar Zabe mai zaman kanta INEC ta soke ayyana Aisha Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa.
INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Lahadi.
Ga cikakken sanarwar a kasa:
"A janyo hankalin Hukumar kan ayyana wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa da Baturen Zabe (REC) ya yi duk da cewa ba a kammala zaben.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Abin da REC din ya aikata ya saba karfin iko na baturen zabe. An soke kuma ba shi da wani tasiri.
"Don haka, an dakatar da cigaba da sanar da sakamakon zaben na ciko.
"An kuma gayyaci Baturen zaben da dukkan masu hannu a lamarin zuwa Hedkwatar INEC da ke Abuja nan take.
Legit.ng ta fahimci cewa an shiga ruɗani da kace-nace bayan kwamishinan INEC na Adamawa ya sanar da Sanata Aishatu Dahiru Binani, a matsayin wacce ta ci zaɓen Adamawa.
Kwamishinan ya bayyana haka ne ana dab da dawowa ci gaba da tattara sakamakon cikon zaɓen gwamnan wanda aka gudanar ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023.
Har zuwa daren Asabar, INEC ta iya kammala tattara sakamakon kananan hukumomi 10 daga cikin 20 da aka gudanar da cikon zaɓen, ta ɗage aikin zuwa karfe 11:00 na safiyar Lahadi.
A halin yanzun, INEC ta soke sanarwan da REC ya yi ta kuma umarci ya tafi Abuja domin jin dalilinsa na ɗaukar wannan mataki.
A wani labarin kuma mun haɗa muku Jerin Matan Arewa Da Suka Ciri Tuta A Siyasar Najeriya Da Maza Suka Yi Kaka-Gida
Ko a zaben bana 2023, ana kiki kaka da Sanata Aishatu Binani a kujerar gwamnan jihar Adamawa, lamarin da a yanzu ya ɗauki sabon salo.
Asali: Legit.ng