APC Ce Gaba a Kebbi, PDP a Adamawa: Yadda Sakamakon Zaben Gwamnonin Yake Kafin Zaben Ciko

APC Ce Gaba a Kebbi, PDP a Adamawa: Yadda Sakamakon Zaben Gwamnonin Yake Kafin Zaben Ciko

Nan ba da jimawa ba masu zabe za su yi tururuwan fitowa a Adamawa da Kebbi don kada kuri'unsu ga yan takarar gwamna da za su fafata a zaben cike gurbi na yau Asabar, 15 ga watan Afrilu.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta raba kayan zabe zuwa rumfunan da zabe zai gudana.

Aishatu Binani da Umar Fintiri
APC Ce Gaba a Kebbi, PDP a Adamawa: Yadda Sakamakon Zaben Gwamnonin Yake Kafin Zaben Ciko Hoto: Petra Abayomi Akinti Onyegbule, Adamawa State Government
Asali: Facebook

Sai dai kuma, gabannin zaben, ya kamata mu tunatar da ku game da kuri'un da kowani dan takara da ke cikin zaben yake da shi a yanzu haka.

Jihar Adamawa

Za a fafata a zaben ne tsakanin gwamna mai ci kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ahmadu Fintiri, da yar takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben Cike Gurbi Na 2023: Jerin Manyan Yan Takara Da Kallo Ke Kansu

Duba yawan kuri'un da suke da shi a yanzu haka a kasa:

Ahmadu Fintiri (PDP) - Kuri'u 421,524

Sanata Aisha Dahiru Binani (APC) - Kuri'u 390,275

Jihar Kebbi

A jihar Kebbi, zaben cikon zai kasance tsakanin dan takarar APC, Nasiru Idris da dan takarar PDP, Janar Aminu Bande ne.

Dubi yawan kuri'un da kowannensu yake da shi a yanzu haka:

Nasiru Idris (APC) - kuri'u 388,258

Janar Aminu Bande (PDP) - kuri'u 342,980

Zaben cike gurbi: INEC ta fara rabon kayan zabe a jihar Adamawa

A baya mun ji cewa hukumar zabe a jihar Adamawa ta fara rabon kayayyakin zaɓe a wuraren da za a gudanar da zaɓen cike gurbi na gwamnan jihar a ranar Asabar.

Hukumar INEC ta bayyana zaben gwamnan jihar na watan Maris a matsayin wanda bai kammalu ba, domin yawan katin zaben da aka karba a wuraren da aka soke zaben ya zarce tazarar da aka bayar a zaben.

Kara karanta wannan

Jerin Jihohi 23 da Duka Mazabun da INEC Za Ta Karasa Gudanar da Zabe a Makon Nan

Fafatawar dai ta fi zafi ne a tsakanin Sanata Aishatu Binani ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da gwamnan jihar mai ci yanzu, Ahmadu Umar Fintiri na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), wanda ya ke kan gaba da kuri'u 30,000.

Kwamishinonin zaben biyu hukumar INEC na kasa, Farfesa Abdullahi Abdulzuru da Dr. Baba Bola, suna wajen domin sanya ido kan yadda rabon kayayyakin zaben yake gudana a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng