Zaben Cike Gurbi: Fintiri, Binani Da Sauran Manyan Yan Takara Da Kallo Ke Kansu
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) za ta gudanar da cikon zaben gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu.
Hukumar za ta kuma gudanar da zabukan ciko na kujerun yan majalisun tarayya da na jiha guda 94.
Ga wasu daga cikin manyan yan takarar da za su fafafata a zaben.
Ahmadu Fintiri
Ahmadu Fintiri ya kasance gwamnan jihar Adamawa mai ci kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan na jihar Adamawa mai ci ya samu jimilar kuri'u 421,524 a zaben ranar 18 ga watan Maris amma ba a ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba saboda kuri'un da aka soke sun fi tazarar da ke tsakaninsa da yar takara ta biyu.
Aisha Dahiru
Sanata Aisha Dahiru, wacce aka fi sani da Binani ta kasance yar takarar gwamna a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.
Ta samu kuri'u 390,275 a zaben baya, tana mai bin Fintiri da tazarar kuri'u fiye da 30,000.
Za a samu wanda zai lashe zaben tsakanin Fintiri da Binani a yau Asabar, 15 ga watan Afrilu.
Nasiru Idris
Nasiru Idris shine dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Kebbi.
Kafin a ayyana zaben gwamnan jihar Kebbi a matsayin wanda bai kammala ba, Idris da APC suna da kuri'u 388,258.
Janar Aminu Bande
Janar Aminu Bande ya kasance dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Kebbi. Zai shiga zaben cike gurbi da kuri'u 342,980.
Ana sanya ran zaben cike gurbin zai karkata ne tsakanin Bande da Idris.
Ganduje ya ware miliyoyi don daukar nauyin yan daba a zaben ciko, Abba Gida-Gida
A wani labarin kuma, zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida ya zargi Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da ware miliyoyin naira don daukar hayar yan daba yayin zaben ciko da za a yi a ranar Asabar, 15 ga watan Afrilu.
Abba ya ce an rabawa shugabannin kananan hukumomin tsaba na miliyoyi domin daukar wadanda za su tarwatsa zaben da za a yi.
Asali: Legit.ng