Zamu ci gaba da rike majalisar dokokin Filato har sai an samu sulhu, CP

Zamu ci gaba da rike majalisar dokokin Filato har sai an samu sulhu, CP

  • Jami'an hukumar yan sanda sun hana yan majalisu shiga zauren majalisar dokokin jihar Filato
  • Tun ranar 5 ga watan Afrilu, yan sanda suka kwace zauren majalisar kuma kwamishina ya ce a haka za'a ci gaba da tafiya
  • CP ga shawarci ɗaukacin mazauna jihar da karsu sake wani ya yi amfani da su wajen ta da zaune tsaye da nufin cimma burinsa

Plateau - Har yanzun zauren majalisar dokokin jihar Filato na karkashin ikon rundunar 'yan sanda kuma jami'ai sun hana mambobin majalisar shiga ciki domin gujewa ɓarkewar rikici.

Kwamishinan yan sandan jihar, Bartholomey Onyeka, ya ce zauren majalisar zai ci gaba da zama a hannunsu har sai lokacin da komai ya dawo ka hanya tsakanin 'yan majalisun.

Zauren majalisar dokokin jihar Filato.
Zamu ci gaba da rike majalisar dokokin Filato har sai an samu sulhu, CP Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Ya ce sun mamaye zauren ne bayan samun wasu bayanan sirri da ke nuna akwai barazanar rasa rai da kadarori, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Sojoji Sun Murkushe Kasurgumin Dan Bindigar Kaduna, Isiya Danwasa

CP Onyeka ya faɗi haka ne ranar Talata yayin da yake hira da manema labarai a Jos kan dalilin da yasa dakarun 'yan sanda suka kwace iko da zauren majalisar tun ranar 5 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ya ce hukumar yan sanda ta samu rahoton cewa da yuwuwar kai hari zauren majalisat wanda ka iya ta da yamutsi da karya doka da oda.

Ya ce hukumar 'yan sanda ta samu rahoto a Soshiyal midiya cewa tsohon kakakin majalisar, Abok Ayuba, wanda mambobi suka tsige ranar 28 ga watan Oktoba, 2021, ya samu umarnin Kotu na komawa kan kujerarsa.

Daily Trust ta rahoto Onyeka na cewa:

"Da fari mun bar zauren majalisar har mambobi sun fara zuwa suna shiga gabanin hukuncin Kotu amma sai muka samu bayanan sirri cewa wasu gurbatattu sun shirya shiga cikin majalisar ta kowane hali."

Kara karanta wannan

Tahajjud: An haramtawa Limamai karanta Qur'ani ta waya a sallolin watan Ramadana

"Da kaina na ɗauki matakin kwace zauren majalisar domin tabbatar da majalisar dokokin jiha ta zauna lafiya da kuma guje wa rasa rai da dukiyoyi."

Bugu da ƙari, ya yi bayanin cewa bisa la'akari da bayanan sirri, hukumar ta gayyaci wasu 'yan majalisu tare da lauyoyinsu zuwa ofishinsa kana ya basu shawarin su guji duk wani abu da zai kawo hatsaniya.

Haka zalika kwamishinan 'yan sandan ya yi kira ga mazauna jihar Filato da karsu yarda wani mutum ya yi amfani da su don cimma wasu burikansa na son rai.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Goyi Bayan Zanga-Zangar PDP, Ya Ce Bai Aminta da INEC Ba

Gwamnan jihar Ribas ya ce zanga-zangar da har yau mambobin jam'iyyar PDP ke gudanarwa a ofishin INEC tana kan hanya.

Wike ya yi ikirarin cewa duk wasu hujjoji da yan adawa ke tattara wa zuwa Kotun zaɓe yana tattare da su a na'urar aje bayanai.

Kara karanta wannan

Gwauro-Gwauro: An Haramta Wasan Tashe A Jihar Kano, 'Yan Sanda Sun Ɗauki Mataki Mai Tsauri

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262