Ministan Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Shugaba Buhari Ya Cikawa 'Yan Najeriya

Ministan Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Shugaba Buhari Ya Cikawa 'Yan Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cika alƙawarin da ya yiwa ƴan Najeriya kan zaɓe
  • Ministan Buhari, Lai Mohammed shine ya bayyana hakan inda yace ƴan Najeriya basu bin Buhari bashin gudanar da sahihin zaɓe
  • Lai Mohammed yayi ƙarin haske kan dalilan da ya sanya zaɓen bana ya kasance sahihi

Abuja- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya cika alƙawarin da ya ɗauka na gudanar da sahihin zaɓe a ƙasar nan.

Ministan watsa labarai da al'adu, Lai Mohammed, shine ya bayyana hakan inda yace shugaban ƙasar zai bar tarihin yin ingantaccen zaɓe a shekarar 2023. Rahoton Vanguard

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da wasu gidajen watss labarai na ƙasashen waje.

Lai Mohammed
Ministan Ya Buhari Ya Bayyana Wani Muhimmin Alkawari Da Shugaba Buhari Ya Cikawa 'Yan Najeriya Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Yace domin cika alƙawarin da shugaban ƙasan yayi na dawo da martabar zaɓe a ƙasar nan, ya yanke shawarar ƙin fifita wata jam'iyya ciki har da jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress, APC, a lokacin zaɓen. Rahoton Punch

Kara karanta wannan

Ta Fashe An Ji: An Fallasa Mutanen da Tinubu Zai Naɗa a Gwamnatinsa Duk da Ba 'Yan APC Bane

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Lai yace a lokacin zaɓen, shugaba Buhari ya tabbatar da cewa babu wanda yayi amfani da jami'an tsaro domin yin maguɗi, inda aka tabbatar da cewa babu wani ko wata jam'iyya da ta samu fifiko.

A kalamansa:

“Hujjar cika wannan alƙwarin nasa shine jam'iyyar shugaban ƙasa ta faɗi zaɓen shugaban ƙasa a jihar sa ta Katsina."
“Haka kuma, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya faɗi a jihar sa ta Legas, yayin da shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya faɗi a jihar sa ta Nasarawa a hannun Labour Party."
“Darekta janar na kamfen ɗin shugaban ƙasa na jam'iyyar mu shi ma ya sha kashi a hannun PDP a jihar Plateau."
“Babu abinda ya ƙara tabbatar da sahihancin waɗannan zaɓukan face yadda ba ayi maguɗi ba a jihohin da manyan jiga-jigan mu suka fito ba."

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana, Dan Takarar Gwamnan APC Ya Tono Kulla-Kullar Da Ake Shirya Masa Don Hana Shi Zuwa Kotu

Ministan ya kuma ƙara da cewa jam'iyyar APC ta sha kashi a jihohi huɗu waɗanda ke da yawan mafiya ƙada ƙuri'u a zaɓen, Katsina, Kano, Kaduna da Legas duk kuwa da cewa jihohin suna ƙarƙashin ikon jam'iyyar ne.

Yaron Ganduje Ya Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Kashin Da Ya Sha a Zabe

A wani labarin na daban kuma, yaron gwamnan Kano, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar rashin nasarar da yayi a zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya.

Umar Abdu Umar ya sha kashi ne a takarar da yayi na kujerar ɗan majalisar wakilai ta tarayya a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng