"Mara Amfani" Ganduje Ya Fusata da Kalaman Abba Gida-Gida Na Hana Shi Bashi
- Gwamnan Kano ya fusata da kalaman Abba Gida-Gida, ya ce maganganun da yake alama ce ta rashin sanin shugabanci
- Dakata Abdullahi Ganduje ya ce shawarin da zababben gwamnan yake bayarwa ba su da amfani
- Wannan na zuwa bayan sabon gwamnan ya gargaɗi masu baiwa gwamnatin Kano bashi su dakata
Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki zaɓaɓɓen gwamna, Abba Kabir Yusuf, bisa kalaman da ya yi a baya-bayan nan kan ciyo bashi.
Ganduje ya kira kalaman gwamna mai jiran gadon da, "Mara tushe" da kuma alama ce dake nuna bai san inda ya dosa ba, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida ya shawarci masu baiwa gwamnatin Ganduje Bashi su dakata kuma ya gargaɗi masu gini a filayen gwamnati su shiga taitayinsu.
Ganduje ya maida martani
Ganduje ya yi martani kan kalaman ne yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Asabar jim kaɗan bayan kammala taron Addu'o'i da rokon Allah ya taimaki shugaban masa mai jiran gado, Bola Tinubu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
"Wannan babbar alama ce a zahiri da ke nuna shugabancinsu ba shi da manufa saboda irin waɗannan shawarin ba su da amfani kuma ba su da tushe."
"Yana magana da jiji da kai kamar yanzu haka shi ne gwamna Kano. Muna masa fatan ya yi abun kirki amma abinda muke so ka gane zamu kalubalanci wannan nasarar ta wucin gadi a Kotun sauraron karar zaɓe."
"Amma ka ga mutum ya fara magana barkatai irin waɗan nan, ai kai zaka wa kanka alkalancin cewa bai fara da kafar dama ba."
Abba Gida-Gida ya fara magana kan harkokin gwamnatin Kano mako ɗaya bayan INEC ta ce shi ne ya lashe zaɓen ranar 18 ga watan Maris, 2023, wanda Ganduje yace a haɗu a Kotu.
Yadda zan kawo karshen ta'addanci a Katsina - Dikko Raɗda
A wani labarin kuma Zababben Gwamna Zai Bullo Da Sabuwar Dabarar Yakar Yan Ta'adda a Katsina
Gwamna mai jiran gado a jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, ya sha alwashin sharewa Katsinawa hawayensu na tsawon shekaru.
Asali: Legit.ng