"Akwai Yiwuwar Tinubu Ya Ba Ni Mukamin Minista a Gwamnatinsa" – Gudaji Kazaure
- Hon. Muhammed Kazaure Gudaji, ya fara hararar kujerar minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu mai kamawa
- Dan majalisar mai wakiltan mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi na jihar Jigawa ya ce yana sa ran Tinubu zai ba shi Minista ko wani babban kwamiti ya jagoranta
- Ya kuma bayyana cewa za su bankado kudaden da za a yi amfani da su wajen tafiyar da gwamnati mai kamawa ba tare da an ciyo bashi ba
Dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa, Yankwashi na jihar Jigawa a majalisar wakilai, Muhammed Gudaji Kazaure, ya nuna yakinin cewa zai samu babban kujera a gwamnatin zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Kazaure ya bayyana cewa yana sanya ran Tinubu zai nada shi mukamin minista ko kuma ya bashi wani babban kawamiti da zai bankado kudade a kasar.
Za mu yi aiki don samo kudaden da za a tafiyar da gwamnati mai kamawa, Kazaure
Ya kuma jaddada cewa yana sa ran da wannan aiki da zai yi wa gwamnati mai kamawa za a yi nasarar samun kudaden aiki a kasar ta yadda ba sai an ciyo bashi ba harma a kai ga biyan basussukan da ake bin kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A wata hira da ya yi da DCL Hausa, dan majalisar ya kuma ce zababben shugaban kasar ya ce zai neme shi domin su zauna su tattauna badakalolin da ya bankado a kasar.
"Idan Allah ya yarda ina sa ran Asiwaju zai kira ni, ya bani kwamiti babba ko ya bani minista, ina sa ran haka. Ko ya bani minista ko ya bani kwamiti babba wanda zan ci gaba da wannan aiki inda za mu samo kudin da za a tafiyar da gwamnati ba tare da an sake cin bashi ko an ci bashi ba. Kuma za mu yi kokari mu samo kudin da za a ma biya basussuka da dukka ake bin Najeriya na gida da ma waje da izinin Ubangiji.
Da aka tambaye shi kan ko sun hadu da Tinubu tun bayan da ya ci zabe don tattauna badakalar da ke kasa, Kazaure ya ce:
“Gaskiya na je mun hadu da shi, na yi mai murna mun zauna mun gaisa mun yi maganaganu amma saboda yan murna da suke yawan zuwa kuma da mutane gidan a cike, ana ta murna ana ta zuwa, ba mu samu damar kebewa mun yi wannan magana ba. Amma ya fada mun bayan kwana biyu zai neme ni za mu zauna."
Ga bidiyon hirar tasu a kasa:
Makiyan Najeriya ne ke so a tsige shugaban INEC, Ogah
A wani labari na daban, dan majalisar tarayya, Kwamrad Chinedu Ogah, ya ce makiyan Najeriya ne suke neman a tsige shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, don ya yi kokari a zaben 2023.
Asali: Legit.ng