"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

"An Hada-Kai da INEC, Za a Murde Zaben Gwamna a Jihar Adamawa" Inji Jam’iyyar PDP

  • PDP ta bukaci a sauke babban Kwamishinan hukumar zabe watau REC da ke jihar Adamawa
  • Jam’iyyar hamayya ta na so a gurfanar da Hudu Yunusa Ari bisa zargin shirya magudin zabe
  • Debo Ologunagba ya ce jami’in ya hada-kai da Aisha Dahiru Binani domin ayi wa PDP murdiya

Abuja - A ranar Litinin, jam’iyyar PDP ta fitar da jawabi ta bakin Kakakinta, Debo Ologunagba domin bayyana matsayarta a kan zaben Adamawa.

Kamar yadda jawabin da aka fitar a shafin Twitter ya nuna, PDP ta na zargin Hudu Yunusa Ari da kokarin shirya magudi a zaben Gwamnan jihar.

Honarabul Ologunagba ya jefi Malam Hudu Yunusa Ari da zargin yunkurin taba sakamakon zaben da aka soma a ranar 18 ga watan Maris 2023.

Vanguard ta rahoto Sakataren yada labaran PDP na kasa ya na cewa sun san jami’in na INEC yana yi wa Sanata Aisha Dahiru Binani aiki ne a Adamawa.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Zargin Magudi a Fufore

Bugu da kari, jam’iyyar ta tuhumi Hudu Ari da hada-kai wajen yin magudi a karamar hukumarFufore domin jam’iyyar APC ta iya lashe zaben Gwamna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A madadin shugaban PDP na kasa, Ologunagba ya yi kira ga INEC ta guji shirya wani magudi.

Gwamnan Adamawa
Gwamna Ahmadu Fintiri a ofis Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

The Cable ta ce Iyorchia Ayu ya yi ikirarin sakamakon zaben da suke da su daga wakilansu, sun tabbatar masu da Ahmadu Fintiri ya lashe zabe.

"Ahmadu Fintiri ne a kan gaba da kuri’u 31,299 da ka kada, yana gaban Sanata Aisha Binani wanda ta dage sai an yi wa mutanen Adamawa magudi.
Za a iya tunawa PDP ta ankarar da ‘Yan Najeriya kan yadda APC da wasu bata-garin jami’an INEC suka so a koma tattara zaben daga Yola zuwa Abuja.
Wannan zai ba jami’in tattara akamakon zaben INEC damar sanar da ‘yar takarar jam’iyyar APC da ta sha kashi a matsayin wanda tayi nasara a zaben.

Kara karanta wannan

Maganar Tsige Shugaban PDP Tayi Karfi, Rikicin Jam’iyya Ya Cigaba da Jagwalgwalewa

Da haka ya gagara, sai APC ta hurowa INEC wuta a soke sakamakon zabe a rumfuna 69 da sunan an kada kuri’un da sun wuce kima, saboda ayi magudi."

- Debo Ologunagba

PDP ta na so a daure REC

Jawabin ya kara da cewa ana so a soke kuri’un kananan hukumomi 21 da aka tatara tun tuni. PDP ta ce ta samu hujja da ke nuna rashin gaskiyar Kwamisina.

Ologunagba yake cewa an ji Binani ta na tunkaho da cewa sai yadda tayi da Hudu Yunusa Ari.

A karshe jam’iyyar PDP ta bukaci INEC ta sauke Ari daga kujerarsa ta Kwamishina, ta damka shi a hannun ‘yan sanda domin ayi bincike, sai a kai shi kotu.

Zaben jihar Sokoto

A makon da ya gabata, an ji labarin yadda Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto ya yi wa Dr. Lawal Dauda Dare nasiha yayin da yake shirin shiga ofis a Zamfara.

Kara karanta wannan

Kasar Ingila ta Kakaba Takunkumi a kan ‘Yan Siyasa 10 a Najeriya Saboda Kalamansu

Malamin ya fadawa zababben Gwamnan na jihar Zamfara ya jawo na kwarai, ya dauko masu fadan gaskiya, ya rike zikiri kuma ya nemi taimakon Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng