Yanzu Yanzu: Yan Daba Sun Cinna Wuta a Gidan Mawaki Rarara

Yanzu Yanzu: Yan Daba Sun Cinna Wuta a Gidan Mawaki Rarara

  • Wasu da ake zargin 'yan bangar siyasa ne sun cinna wuta a gidan fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara
  • Yan daba sun bakkawa gidan Rarara da ke jihar Kano wuta a safiyar yau Litinin, 20 ga watan Maris
  • Rarara dai ya kasance dan gani-kashenin jam'iyyar APC mai mulki wacce ta sha kaye a zaben gwamnan jihar na 2023

Kano - Kasa da awa daya bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, wasu yan daba da ba'a san ko su wanene ba sun sanya wuta a gidan shahararren mawakin siyasan nan, Dauda Kahutu Rarara.

Rarara dai ya karkata ne wajen yi wa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) kamfen, inda ya yi wakoki a gangamin kamfen jam'iyyar daban-daban.

Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara
Yanzu Yanzu: Yan Daba Sun Cinna Wuta a Gidan Mawaki Rarara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

A cewar wani ganau wanda ya kasance mazaunin yankin, Yusuf Abdullahi, yan daban sun farmaki gidan mawakin sannan suka fara lalata muhimman abubuwa kafin suka cinna wa gidan wuta.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Hana FitaDaga Safe Har Dare

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, yan mintuna bayan nan, an tattaro cewa yan sanda sun tarwatsa yan daban amma dai wutan ya ci gaba da ci yayin da ake jiran isowar yan kwana-kwana.

Abdullahi ya ce:

"Babu abun da kake jiyowa sai karar fashewar abubuwa daga gidan yayin da wutan ke ci gaba da lalata kayayyaki."

Ga bidiyon gidan da ke ci da wuta a kasa:

Yan sanda sun yi kame

Har ila yau, a wani bidiyo da jaridar Daily Trust ta wallafa, an gano jami'an tsaro suna kame inda suka cafke wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a harin da aka kai gidan mawakin.

Kalli bidiyon a kasa:

Gwamnatin jihar Kano ta saka dokar hana fita

A gefe guda, mun ji cewa bayan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita wanda zai yi aiki daga safe har dare.

Kamar yadda kwamishinan labarai na jihar, alam Muhammad Garba, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Litinin, 18 bga watan Maris, an saka dokar ne domin hana barkewar rikici a jihar wacce ta riga ta dauki dumi saboda zaben gwamna da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: