Ahmed Aliyu Na APC Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Sokoto

Ahmed Aliyu Na APC Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Sokoto

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ayyana dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Ahmed Aliyu, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto.

Mista Aliyu ya samu kuri’u mafi rinjaye don haka aka sanar da shi a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben na ranar Asabar, 18 ga watan Maris.

Aliyu ya samu jimilar kuri’u 453,661 wajen doke babban abokin hamayyarsa, Saidu Umar na PDP wanda ya samu kuri’u 404,632.

Karamar hukumar Wamakko

APC 36233

PDP 27642

Karamar hukumar Tambuwal

APC 29489

PDP 32779

Karamar hukumar KEBBE

APC;14,902

PDP:14,619

Karamar hukumar Sokoto ta arewa

APC:35,333

PDP; 33,190

Karamar hukumar Sokoto ta kudu

APC:37,114

PDP:33,363

Karamar hukumar Gada

APC:19,969

PDP:18,434

Karamar hukumar Gudu

APC: 12,118

PDP: 10,718

Karamar hukumar Illela

APC: 23,484

PDP: 19,169

Karamar hukumar Goronyo

APC 16,567

PDP 17,323

Karamar hukumar Dange-Shuni

APC 22,690

PDP 18,506

Karamar hukumar Silami

APC 9,983

PDP 10,885

Karamar hukumar Sabon Birni

APC - 26,884

LP- 2

PDP - 20,680

NNPP- 4

Karamar hukumar Shagari

APC - 14,264

LP- 11

PDP - 13,893

NNPP- 5

Karamar hukumar Kware

APC – 18,644

PDP – 18,161

Karamar hukumar Tangaza

APC – 16,254

PDP – 9,705

Karamar hukumar Bodinga

APC – 18,986

PDP – 16,440

Karamar hukumar Tureta

APC – 9,831

PDP – 10,045

Karamar hukumar Rabah

APC – 12,759

PDP – 11,120

Karamar hukumar Gwadabawa

APC – 19,036

PDP – 16,652

Karamar hukumar Isa

APC – 13,632

PDP – 15,117

Karamar hukumar Yabo

APC – 14,729

PDP – 12,014

Karamar hukumar Wurno

APC – 17,350

PDP – 13,099

Karamar hukumar Binji

APC – 13,410

PDP – 11,078

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng