Yanzu Yanzu: Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Imo

Yanzu Yanzu: Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Imo

  • Yan sanda sun kubutar da jami'an INEC 19 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Imo
  • Wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace jami'an zaben na wucin gadi a hanyarsu ta zuwa mazabun da za su yi aiki
  • Sai dai ba a yi nasarar kwato kayayyakin zabe da na'urorin BVAS daga maharan ba

Imo - Jami'an rundunar yan sanda a jihar Imo sun ceto jami'an hukumar zabe na wucin gadi guda 19 da aka yi garkuwa da su a safiyar ranar Asabar a jihar.

Hukumomin INEC a jihar ne suka tabbatar da ci gaban kamar da gidan talbijin na Channels ta rahoto.

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yanzu Yanzu: Yan Sanda Sun Ceto Jami’an INEC 19 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Imo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewar mahukunta, jami'an zaben 19 na a hanyarsu ta zuwa rumfunan zabensu mabanbanta a gudunmar Ugbelie 06 a karamar hukumar Ideato ta kudancin jihar Imo lokacin da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan daba na yiwa jama'a barazar ko su zabi APC ko su su dauki wani mataki a wata jiha

INEC ta tabbatar da ceto jami'anta 19 da sace a Imo

Mai magana da yawun hukumar INEC, Chinenye Chijioke-Osuji, ya ce an ceto mutanen ne bayan wani kira mai cike da damuwa da kuma ba jami'an tsaron bayanai game da lamarin. Nan take sai suka shiga aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta kara da cewar koda dai an ceto su, ba a samu damar kwato kayayyakin zaben da suka hada da BVAS da sauransu ba, rahoton Vanguard.

Yan bindiga sun kwace tare da kona kayan zabe a Bayelsa

A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa wasu tsagerun yan bindiga sun farmaki kayayyakin zabe a yankin mazabar Ogbia da ke jihar Bayelsa a safiyar Asabar, 18 ga watan Maris.

Maharan sun kwace tare da kona kayayyakin zaben na majalisar dokokin jihar kasancewar sai a watan Nuwamba za a yi zaben gwamna a jihar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kwace Kayan Zabe Sun Kona a Wata Jihar Kudu, Jami'an INEC Sun Tsere

Wannan hari da suka kai ya tilastawa jami'an zabe gaggauta barin garin inda suka koma Yanagoa, babban birnin jihar don tsira da ransu.

Da take tabbatar da lamarin, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC ta bakin kakakinta a jihar, Mista Wilfred Ifogah, ta ce za ta fitar da jawabi dangane da a'lamarin zuwa nan gaba kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng