DSS Sun Kama Mutum 2 Kan Shirin Haddasa Rikici Yayin Zaben Gwamnan Kano

DSS Sun Kama Mutum 2 Kan Shirin Haddasa Rikici Yayin Zaben Gwamnan Kano

  • Jami'an hukumar DSS sun yi ram da Sharu Abubakar Tabula da Isma’il Iliyasu Mangu a jihar Kano
  • DSS na zargin wasu matasa biyu da kokarin tayar da zaune tsaye yayin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar a jihar Kano
  • Matasan sun saki wasu faifan bidiyo dauke da sakonni masu hatsari suna masu bukatar magoya bayansu da su farmaki abokan hamayya

Kano - Rundunar tsaron farin kaya (DSS) ta kama wasu mutum biyu bisa zarginsu da shirin haddasa rikici a yankunan jihar Kano, jaridar The Cable ta rahoto.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar DSS, Peter Afunanya, ne ya sanar da batun kamun nasu a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 16 ga watan Maris a Abuja.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 Bayan Rasa Rayyuka 17, Yan Ta'adda Sun Sake Kai Kashe Mutum 10 A Sabon Hari

Mutanen da DSS ta kama a Kano
DSS Sun Kama Mutum 2 Kan Shirin Haddasa Rikici Yayin Zaben Gwamnan Kano Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

A cewar Afunanya, wadanda ake zargin, Sharu Abubakar Tabula da Isma’il Iliyasu Mangu sun nadi sakonni daban-daban sannan suka yada su ta shafukan soshiyal midiya da dama, rahoton Daily Trust.

Cikakken jawabin hukumar DSS game da shirin kai hari Kano

Afunanya ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A cikin wadannan sakonni masu hatsari, musamman suka yada wasu muradai na siyasa sannan suka yi kira ga magoya bayansu da su farmaki masu adawa da su.
"Wadanda ake zargin sun kuma yi kira ga farmakar jami'an tsaro a yayin zaben gwamna da na yan majalisa da za a yi a ranar Asabar a jihar.
"Wata jam'iyyar siyasa a Kano ta yi barazanar shirya gangami a birnin sakamakon hare-haren da ake shirin kaiwa.
"Yayin da hukumar ke jan hankalin jama'a game da wannan mataki da ake kitsawa wanda baya bisa doka, ta yi kira ga jam'iyyar da abun da shafa da ta janye kudirinta ko kuma ta shirya fuskantar abun da zai biyo baya.

Kara karanta wannan

Dubu Wasu Yan Fashi Da Makami Sanye Da Kayan Sojoji Ya Cika, Sun Shiga Komadar Yan Sanda

"Hukumar DSS ba za ta zura ido tana kallon miyagun mutane ko kungiyoyi su tarwatsa zaman lafiya da tsaron jihar ba.
"Ya kamata shugabancin jam'iyyar ya ja hankalin mambobinsa sannan ya bukace su da su janye daga gudanar da abun da ka iya karya doka da oda a Jano da kewayenta kafin, yayin da bayan zaben da ake shirin yi."

Afunanya ya ce DSS ta hada kai sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cikakkentsaro don yin zabe cikin nasara a ranar Asabar.

Ban yi wa kowa barazana da kisa ba, Jamilu Gwamna

A wani labarin kuma, jigon jam'iyyar APC a jihar Gombe, Jamilu Gwamna ya karyata zargin cewa yana yi wa al'ummar jihar barazana da kisa gabannin zaben gwamnoni a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: