Jerin 'Yan Takarar da Aka Raina, Waɗanda Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni
Sakamakon tsaikon da aka samu daga rashin saita na'urorin BVAS a kan lokaci, INEC zata gudanar da zaben gwamnoni a jihohin Najeriya ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Kawo yanzun kowane ɗan takarar gwamna da jam'iyyarsa sun maida hankali wajen yakin neman zabe domin jawo ra'ayin masu kaɗa kuri'a su zaɓe su ranar Asabar mai zuwa.
Yayin da ake ganin jam'iyyu biyu ne manya, Legit.ng Hausa ta zakulo muku wasu yan takarar gwamna da ake ganin ba zasu kai labari ba, kuma da yuwuwar su ba da mamaki.
1. Ɗan takarar gwamnan NNPP a Bauchi
Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ayyana Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya, Sanata Halliru Jika, a matsayin ɗan takararta na gwamna a jihar Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Jika ne shugaban kwamitin kula da harkokin 'yan sanda na majalisar Dattawa kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi.
Da fari ya nemi tikitin takarar gwamna a inuwar APC amma ya sha kaye hannun tsohon shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar. Bayan haka ya sauya sheƙa zuwa NNPP.
Sanata Jika ya jaddada yakininsa cewa shi ne zai zama gwamnan jihar Bauchi na gaba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
2. Ɗan takarar LP a Legas
Daga cikin abubuwan ban mamakin da suka faru a zaben shugaban kasa har da sakamakon da ya fito daga jihar Legas. Labour Party ta doke APC mai mulki a yawan kuri'u.
Duk da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ɗan Legas ne kuma APC ke mulki a jihar, ana ganin Labour Party (LP) ka iya baiwa mazauna jihar mamaki a zaben gwamna.
Gbadebo Rhodes-Vivour, shi ne ɗan takarar gwamnan LP a Legas bayan ya fice daga PDP. Ana ganin idan APC da PDP suka yi wasa, ɗan takarar ka iya zama zakara a zaben ranar Asabar.
3. Ɗan takarar gwamnan LP a Delta
Jihar Delta na hannun PDP a yanzu haka karƙashin gwamna Ifeanyi Okowa, abokin takarar Atiku a zaben shugaban kasan da ya gabata ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kamar yadda Obi ya ba da mamaki a sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Delta, ɗan takarar gwamnan LP, Ken Pela, ka iya zama zakara a zaben gwamna mai zuwa.
A cewar Mista Ken Pela, mutane Delta sun kagara ranar zabe ta zo su ɗauki fansa kan manyan jam'iyyu biyu watau APC da PDP, rahoton Vanguard ya tabbatar.
A wani labarin kuma Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ya Janyewa Dan Uwan Gwamnan jam'iyyar APC
Ana ta yaɗa cewa mai neman zama nataimakiyar gwamna a inuwar APC a jihar Ebonyi ta yi murabus daga takara saboda rashin lafiya.
Sakataren APC na jihar ya karyata labarin, a cewarsa yar takarar na da cikakkiyar lafiya kuma ta shirya tsaf.
Asali: Legit.ng