Majalisa Ta 10: Ohanaeze Ndigbo Ta Goyi Bayan Gwamna Umahi Ya Zama Shugaban Majalisar Dattawa
- Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta ayyana goyon bayanta ga Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi don ya zama shugaban majalisar dattawa
- Kungiyar dattawan kudu maso gabas ta ce zamowar Umahi shugaban majalisar dattawa zai tabbatar da daidaito da adalci ga yan Ibo
- Hakazalika wata mai sharhi kan harkokin jama'a, Cham Faliya Sharon, ta nemi a baiwa Ahmed Idris Wase kakakin majalisar wakilai
Gabannin kafa majalisar dokokin tarayya ta 10, an bayyana Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi a matsayin wanda ya fi cancanta da zama shugaban majalisar dattawa.
Kungiyar dattawan Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 12 ga watan Maris, Daily Trust ta rahoto.
A cikin sanarwar, babban sakataren kungiyar Ohanaeze Ndigbo, Mazi Okechuwu Isiguzor ya ce domin yi wa kudu maso gabas adalci da daidaito, ya kamata yankin ya samar da shugaban majalisar dattawa.
Isiguzoro ya kara da cewar idan har aka cika wannan bukata tasu, zai kawo hadin kai sannan mutanen yankin Inyamurai za su ga cewa ana yi da su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar The Guardian ta nakalto wani bangare na sanarwar na cewa:
"Don ra'ayin hadin kai, don tabbatuwar jajircewar Umahi na tabbatar da Najeriya daya, ababen more rayuwa da ci gaban yan adam, da kuma muradin Inyamurai da kuma bukatar karfafa daddiyar muradinmu na ganin daya daga cikinmu ya zama shugaban kasa a gaba, muna neman goyon bayan kowa don nada Umahi a matsayin shugaban majalisar dattawa na gaba."
Baya ga wannan kira na kungiyar inyamuran, kwamitin aiki na jam'iyyar All Progressives Congress a Ebonyi ta bukaci shugabancin jam'iyyar na kasa da ya duba yiwuwar ba Umahi wannan mukami.
Kwamitin wanda ya samu jagorancin Cif Stanley Okoro Emegha, wadanda suka je Abuja a ranar Lahadi, ya kuma yi kira ga APC da ya mika kujerar kakakin majalisa zuwa arewa ta tsakiya.
Wase don zama kakakin majalisar wakilai
A halin da ake ciki, wata mai sharhi kan harkokin jama'a mazauniyar Abuja, Cham Faliya Sharon, ta bukaci jam'iyyar da ta marawa takarar mataimakin kakakin majalisa mai ci, Ahmed Idris Wase don zama kakakin majalisar.
"Tun babban zaben 2015 har zuwa yau, babban bangare na yankin arewa maso tsakiya na ci gaba da goyon bayan APC, kuma ya kamata a nuna godiya ga wannan goyon baya da biyayya ta hanyar mika wannan babban kujera zuwa garesu don jam'iyyar ta habbaka da rike matsayinta a yankin."
Mukaman da El-Rufai, Gbajabiamila da sauransu za su iya samu a gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, mun ji cewa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na iya baiwa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ko takwaransa na jihar Kano, Abdullahi Ganduje mukamin sakataren gwamnatin tarayya a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng