Lagas, Delta: Jerin Jihohin Da Peter Obi Ya Lashe a Zaben Shugaban Kasa Na 2023
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta kammala tattara sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.
An tattara sakamakon zaben na kasa a cibiyar taro na kasa da kasa da ke Abuja karkashin jagorancin Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.
Zaben shugaban kasa na 2023: Tattara sakamako na kasa a Abuja
An tattara sakamakon jihohi 36 harda babban birnin tarayya a matakin kasa a Abuja. Sune:
- Jihar Ekiti
- Jihar Kwara
- Jihar Osun
- Jihar Ondo
- Jihar Ogun
- Jihar Oyo
- Jihar Yobe
- Jihar Enugu
- Jihar Lagos
- Jihar Gombe
- Jihar Jigawa
- Jihar Adamawa
- Jihar Katsina
- Jihar Nasarawa
- Jihar Niger
- Jihar Benue
- FCT
- Jihar Akwa Ibom
- Jihar Edo
- Jihar Abia
- Jihar Kogi
- Jihar Bauchi
- Jihar Plateau
- Jihar Bayelsa
- Jihar Kaduna
- Jihar Kebbi
- Jihar Zamfara
- Jihar Kano
- Jihar Sokoto
- Jihar Cross River
- Jihar Delta
- Jihar Ebonyi
- Jihar Anambra
- Jihar Taraba
- Jihar Borno
- Jihar Rivers
- Jihar Imo
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daga cikin jihohin 36 da birnin tarayya da aka lissafa a sama, dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) Bola Tinubu ya lashe 12 yayin da dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, shima ya lashe 12.
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP) shima ya lashe 12 yayin da Rabiu Kwankwaso na New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya lashe jiha daya: Kano.
Zaben shugaban kasar 2023: Jihohi nawa Peter Obi ya lashe:
Zuwa yanzu, Peter Obi ya lashe jihohin da ke kasa bayan tattara sakamako a matakin kasa:
- Jihar Lagos
- Jihar Enugu
- Jihar Nasarawa
- Jihar Ebonyi
- Jihar Abia
- Jihar Delta
- Jihar Anambra
- Jihar Plateau
- FCT
- Jihar Edo
- Jihar Cross River
- Jihar Imo
Bola Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa, INEC
A gefe guda, mun ji cewa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, ta ayyana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Tinubu ya yi nasara ne bayan ya lashe kuri'u mafi rinjaye a babban zaben kasar da ya gudana a fadin jihohi 36 harda babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairun 2023.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng