Yanzu Yanzu: Yan Sanda Sun Kama Alhassan Doguwa a Filin Jirgin Sama Na Kano
- Yan sanda a Kano sun kama shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa
- An yi ram da Ado Doguwa kan zarginsa da hannu wajen a kisan kai da kona sakataroiyar jam'iyyar NNPP
- Jami'an tsaro sun kama shi ne a hanyarsa ta zuwa Abuja a filin jigin sama na Malam Aminu Kano
Kano - Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa yan sanda sun kama shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa.
An kama Doguwa ne kan zargin rawar ganin da ya taka wajen kisan mutane da dama da kona sakatariyar jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a lokacin zaben da aka kammala.
Yan sanda sun tabbatar da cewar akalla mutum uku ne aka kashe lokacin da aka cinnawa sakatariyar kamfen din NNPP a Tundunwada wuta, Daily Trust ta rahoto.
An kona mutum biyu har lahira yayin rikicin da ya barke yayin tattara sakamakon zaben majalisar wakilai na mazabar Doguwa/Tudunwada, wanda aka ayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kama Ado Doguwa a hanyarsa ta zuwa Abuja
Wata majiya abun dogaro a hukumar yan sandan ta sanar da wakilin Daily Trust cewaan kama Doguwa ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano yayin da shirin hawa jirgin sama zuwa Abuja.
Wata majiya ta bayyana cewa rahoto daga shugaban yan sanda a Tudunwada ya bayyana cewa Doguwa da kansa ne ya jagoranci yan daban da suka cinnawa sakatariyar NNPP wuta inda aka kona mutum biyu har lahira.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunata ta ce:
"Ya kuma yi amfani da bindigar dogarinsa wajen harbin mutane da dama. Saboda haka mun kama shi bisa zargin hannu a kisa da kone-kone.
"Yanzu haka yana sashin binciken masu laifi na jihar."
Ba'a samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ba don baya daukar waya.
Ban san ya ake harbi ba don bani da bindiga - Ado Doguwa
Da farko dai Doguwa ya karyata zargin da ake masa a wata zantawa da manema labari yan awanni kafin kama shi sannan ya ce ya ji labarin yan sanda na nemansa amma bai samu gayyata a hukumance ba.
Ya kuma karyata zargin cewa ya harbi mutane da dama a rikicin da ya barke, yana mai cewa shi bai da bindiga kuma bai san yadda ake harbi ba.
Mun dai ji a baya cewa a kona mutane biyu da ransu yayin da rikicin siyasa ta barke aa jihar Kano lokacin zaben shugaban kasa da yan majalisar tarayya.
Asali: Legit.ng