Tsohon ‘Dan Acaba Ya Doke ‘Dan Siyasar Kaduna da Ya Shafe Shekaru 16 a Majalisa
- Jam’iyyar LP ta karbe kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na shiyyar Kaura a jihar Kaduna
- Hon. Gideon Lucas Gwani bai yi nasara a yunkurinsa na komawa majalisar a karo na hudu ba
- Donatus Mathew wanda ya taba zama ‘Dan acaba shi ne ‘dan takaran da ya doke jam’iyyar PDP
Kaduna - ‘Yan acaba sun yi ta murna da farin ciki yayin da wani abokin aikinsu ya lashe kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya a Najeriya.
Rahoto daga Vanguard ya tabbatar da cewa masu sana’ar haya a kan babur sun ji dadin nasarar da takwaransu ya samu a Kudancin Kaduna.
Hukumar zabe na kasa watau INEC, ta ayyana Mista Donatus Mathew a matsayin wanda ya lashe kujerar Kaura a majalisar wakilai na kasa.
Abin ban mamakin shi ne Donatus Mathew ya doke Honarabul Gideon Gwani ne na PDP.
Zaman majalisa ya kare
Gideon Gwani shi ne yake rike da kujerar masu tsawatar da marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya, ya yi shekaru kusan 16 a kujerar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan tsohon ‘dan acaba ne ya kawo karshen zaman Hon. Gwani a majalisar, ya canje shi a mazabar Kauru da ta ke Kudancin jihar Kaduna.

Source: UGC
Leadership ta ce Mathew ya godewa tsofaffin abokan aikinsa na Acaba da kuma masu fatan alheri bayan da INEC ta sanar da nasararsa a jiya.
‘Dan siyasar ya yi wa al’umma godiya da suka gamsu har suka zabe shi, ya yi alkwari za a ga wakilci a wurinsa, yana mai neman hadin-kan jama'a.
‘Dan majalisar mai jiran gado ya yi alkawari zai tafi da duk wadanda suka taimakawa nasararsa. A watan Yunin 2023 zai shiga cikin ofis.
Yadda LP ta karbe Kaura a 2023
Farfesa Elijah Ella wanda shi ne malamin zabe a yankin, ya ce Mathew ya samu kuri’u 10,508, shi kuma ‘dan takaran PDP yana da kuri’a 10, 297.

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar Peter Obi ta ci kujerar majalisar tarayya a wata jihar PDP
Wannan nasara ta tsohon kansilan da aka sani da harkara caba, ta kawo karshen Gideon Lucas Gwani mai neman zuwa majalisa a karo na biyar.
Obi ya ci zabe a Mubi
A yankin Muchalla da ke garin Mubi, an ji labari Peter Obi da jam’iyyar LP sun samu kuri’a 4524 a zaben sabon shugaban kasa da aka yi ranar Asabar.
Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar ya samu kuri’u 1, 864. Kuri’u 340 da 31 kadai ‘yan takaran APC da NNPP su ka samu a yankin na jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng
