Yanzu Yanzu: Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan Ya Ci Zabe

Yanzu Yanzu: Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan Ya Ci Zabe

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ya sake nasara a zaben sanatan Yobe ta arewa bayan shafe shekaru 22 a majalisa
  • Lawan ya lallasa dan takarar jam'iyyar PDP, Ilu Alhaji-Bello, wanda suka fafata a zaben da shi
  • An sha gwagwarmaya tsakanin shugaban majalisar dattawan da Bashir Machina, wanda shine ya lashe zaben fidda gwanin a kotu

Yobe - Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ayyana Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Ibrahim Lawan, a matsayin wanda ya lashe zaben sanata mai wakiltan Yobe ta Arewa.

Baturiyar zabe na yankin Yobe ta arewa, Farfesa Omolola Aduloje daga jami'ar tarayya ce Gashua karamar hukumar Bade ce ta sanar da sakamakon zaben, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Shugaban majalisar dattawa zaune a kujera
Yanzu Yanzu: Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan Ya Ci Zabe Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Lawan ya lallasa dan takarar PDP a Yobe ta arewa

Ta ce Lawan, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu kuri'u 91,318 wajen lallasa dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Ilu Alhaji-Bello, wanda ya samu kuri'u 22,849.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Zaben 2023: Rikici A APC Yayin Da Shugaban Jam'iyya Na Kasa Adamu Ya Gaza Kawowa Wa Jam'iyyarsa Kujerar Sanata A Mazabarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka ta ayyana Lawan a matsayin wanda ya lashe zaben sanata mai wakiltan Yobe ta arewa a kwalejin ilimi na Umar Suleiman da ke Gashua, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

APC ta tsayar da Lawan wanda bai yi takarar zaben fidda gwanin sanata na jam'iyyar ba bayan ya rasa tikitin shugaban kasa.

Sai dai kuma ya yi nasarar zama dan takarar jam'iyyar a kotun koli, bayan sun fafata da Bashir Machina, wanda ya lashe zaben fidda gwani.

Gwamnonin Cross River da Enugu sun fadi zaben sanata

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ungwuanyi da takwaransa na jihar Cross River, Ben Ayade sun sha kaye a zaben sanata da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Ungwuanyi wanda ya kasance dan takarar jam'iyyar PDP a zaben sanata mai wakiltan Enugu ta arewa ya sha kaye a hannun dan takarar Labour Party.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnonin Enugu Da Cross River Sun Fadi Zaben Sanata

Hakazalika, Ben Ayade wanda shine dan takarar APC a Cross River ta arewa ya sha kaye ne a hannun Sanata mai ci, Jarigbe Agom-Jarigbe.

Su dukka biyun za su kammala wa'adin mulkinsu na biyu a matsayin gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel