Peter Obi Ya Samu Nasarar Farko, Ya Lashe Akwatin Zabensa
- Mr Peter Gregory Obi ya samu nasarar farko a zaben bana, ya lashe akwatin da ya kada kuri'a
- Peter Obi ya lallasa abokan hamayyarsa da tazara mai fadi a rumfarsa ya gundumar Agulu
- Har yanzu ana cigaba da tattaro sakamakon zaben kuri'u a runfuna da aka kada a fadin tarayya
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter, ya samu nasara a akwatin da ya kada kuri'a yau a karamar hukumar Anaocha ta jihar Anambra.
Atiku ya kada kuri'arsa a rumfar zabe ta goma sha tara PU019, gundumar Agulu ta biyu, karamar hukumar Anaocha, rahoton TheCable.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Obi wanda ya kada kuri'arsa tare da iyalinsa a akwatin ya lallasa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, Rabiu Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP da kuma Atiku Abubakarna jam;iyyar PDP.
Ya lashe kusan dukkan kuri'un mazabar illa dan takara jam'iyyar APGA wanda ya samu kuri'u 3, sannan Rabiu Kwankwaso na NNPP da ya samu kuri'u 2.
Tinubu da Obi ko kuri'a dyaa basu samu ba.
Kalli sakamakon:
PU019 Agulu 2 ward Anaocha
APC: 0
PDP: 0
LP: 236
NNPP: 2
APGA: 3
Sakamakon Zaben Akwatin Atiku Ya Fito, Ya Lallasa Tinubu da Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasara a akwatin da ya kada kuri'a yau a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Atiku ya kada kuri'arsa a rumfar zabe ta goma sha biyu PU012, Ajiya, gundumar Gwadabawa, karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar.
Atiku wanda ya kada kuri'arsa tare da iyalin a akwatin ya lallasa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, Rabiu Musa Kwankwaso na Jma'iyyar NNPP da kuma Peter Obi na jam;iyyar LP.
Wanda ya biyo masa shine Tinubu wanda ya samu kusan humusin kuri'un da Atiku ya samu.
Kwankwaso kuwa kuri'a 1 tak a samu yayinda Peter Obi ya samu kuri'u 6.
Asali: Legit.ng