Sakamakon Zaben Akwatin Atiku Ya Fito, Ya Lallasa Tinubu da Kwankwaso
- Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasarar farko a zaben bana, ya lashe akwatin da ya kada kuri'a
- Atiku ya lallasa abokan hamayyarsa da tazara mai fadi a rumfarsa ya gundumar Gwadabawa
- Har yanzu ana cigaba da tattaro sakamakon zaben kuri'an da aka kada a fadin tarayya
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasara a akwatin da ya kada kuri'a yau a Yola, babban birnin jihar Adamawa.
Atiku ya kada kuri'arsa a rumfar zabe ta goma sha biyu PU012, Ajiya, gundumar Gwadabawa, karamar hukumar Yola ta Arewa a jihar.
Atiku wanda ya kada kuri'arsa tare da iyalin a akwatin ya lallasa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, Rabiu Musa Kwankwaso na Jma'iyyar NNPP da kuma Peter Obi na jam;iyyar LP.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wanda ya biyo masa shine Tinubu wanda ya samu kusan humusin kuri'un da Atiku ya samu.
Kwankwaso kuwa kuri'a 1 tak a samu yayinda Peter Obi ya samu kuri'u 6.
Kalli sakamakon:
PU012, Ajiya, Gwadabawa ward, Yola north LGA
APC: 57
PDP: 282
LP: 6
NNPP: 1
Karancin Fitowar Masu Kaɗa Ƙuri'u a Kaduna Ya Dame Ni - El-Rufai
A jihar Kaduna kuwa, Malam Nasiru, yayi mamakin yadda aka samu ƙarancin masu ƙada kuri'a a cikin garin Birnin Kaduna.
Gwamnan ya bayyana haka ne sanda yake hira da masu neman labarai, jim kaɗan da hawan sa kan layi domin yin zaɓe a akwati ta 024, dake a mazaɓar Unguwan Sarki, Kaduna.
Gwamnan yace abin takaici ne ace wai wasu akwatunan babu mutane sosai, musamman yadda aka saba gani a lokutan baya.
Asali: Legit.ng