APC Na Zaba, Tinubu Na Ka'dawa: Buhari Ya Nunawa Jama'a Kuri'arsa
- Shugaba Muhammadu Buhari tare da uwargidarsa, Aisha Muhammadu Buhari sun kada kuri'arsu
- Buhari ya dira a mazabarsu dake garin Daura, jihar Katsina da sanyin safiyar Asabar
- Bayan kada kuri'arsa shugaban kasa ya yi hira da manema labarai da suka yi masa tambayoyi
Daura - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kada kuri'arsa da safiyar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023, a mazabarsa dake Daura, jihar Katsina.
Shugaban kasan ya kada kuri'ar ne tare da uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari kuma sun samu rakiyar Ambasada Lawal Kazaure.
Buhari bayan dannawa jam'iyyar da yake goyon baya, ya nunawa jama'a cewa lallai jam'iyyar APC ya ka'dawa kuri'a.
A bidiyoyi da hotunan da suka yadu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, an ga shugaba Buhari lokacin da ya daga kuri'arsa sama yana nunawa mutane.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shahrarriyar yar jarida, Kadaria Ahmed, a tsokacinta kan wannan hoto ta bayyana cewa yin hakan bai hallata a dokar zaben Najeriya ba.
Ta bayyana cewa:
"La'alla saboda halin ake ciki a cikin jam'iyyarsa inda ake rikicin cikin gida saboda akwai rade-radin cewa yana fuska biyu saboda haka yana son nunawa."
Legit Hausa ta ji ta bakin wani lauya wanda ya bayyana cewa wannan abu ya sabawa doka.
Barista Ameen Yusuf ya bayyana cewa tuni yan siyasa na irin haka kuma ba'a daukan mataki kansu.
Yace takardar kuri'a sirri ce shiyasa ake shiga wani dan zagaye domin kada kuri'ar kuma mutum ya jefa cikin akwatin.
A cewarsa:
"Dama sunayi amma dai ya sabawa doka, ai doka cewa tayi kayi a boye shiyasa ake amfani da cubicle."
Da aka tambayesa shin wani mataki ya kamata INEC ta dauka yanzu kan hakan, yace:
"Kawai a kaishi kotu,"
Atiku Abubakar Ya Dira Rumfar Zabensa Don Ka'da Kuri'arsa
A wani labarin irin wannan, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya isa rumfar zabensa don kada kuri'arsa.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya ka'da kuri'arsa a mazabarsa dake Jimeta tare da uwargidarsa, Hajiya Titi Atiku Abubakar.
Atiku ya bada karfin gwiwar cewa shi zai lashe zaben shugaban kasa.
Asali: Legit.ng