Rikici Ya Barke a Mazabar Kwankwaso, Ana Zargin Wata Mota Ta Kwashe Takardun Zabe
Rikici ya barke a gundumar runfunan zaben dake Makarantar GSS Kwankwaso inda wasu matasa suka hana wata mota fita daga wajen.
Matasan na zargin cewa mai motar ya kwashe takardun zabe cikin motarsa kuma yana kokarin guduwa.
Jami'an tsaron dake wajen na kokarin kwantar da kuran amma abin ya ci tura.
Wakilin Legit Hausa dake wajen, Sani Hamza Daudawa ya bayyana cewa:
"Jami'an tsaro na kokarin kwantar da kurar amma a banza saboda mutanen sun lashi takobin sai ya bude bayan motarsa amma ya ki."

Asali: Original
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Asali: Original

Asali: Original
An Damke N2m Na Dan Siyasa Za'a Sayi Kuri'u Da Su A Gombe
Jami'an rundunar 33 Artillery Brigade Operation Safe Conduct dake Alkaleri, jihar Bauchi sun damke wani mutumi dauke tsabar kudi Naira milyan biyu.
Mutumin mai suna Hassan Ahmed ya shiga hannun Sojin yayinda yake hanyar tafiya zuwa Gombe.
Sojojin sun damkeshi ranar Juma'a kuma suka damkashi hannun jami'an hukumar yaki da rashawa ICPC, shiyar jihar Bauchi.
An damke Ahmad dauke da N900,000 na sabbin kudi, da kuma N1.1 million na tsaffin kudi cikin mota kirar Hilux mai lamba JMA 85 AZ.
An gano kudin cikin jaka “Ghana Must Go” dauke da bandirin sabbin duba daya-daya na N600,000; bandir shida na dari biyar na kudi N300,000 sannan yan dari biyu-biyu na tsaffin kudi N1.1 million.
Asali: Legit.ng