Hukumar INEC Ta Dakatar Da Zaben Gobe Na Kujerar Sanatan Enugu East

Hukumar INEC Ta Dakatar Da Zaben Gobe Na Kujerar Sanatan Enugu East

  • Shugaban hukumar INEC ya kira hira da manema labarai domin tattauna halin da za'a shiga gobe
  • Farfesa Mahmoud ya tabbatar da samun labarin kisan dan takarar majalisar dattijai a farkon mako
  • An dage zaben wannan mazaba kuma za'a gudanar tare da na gwamnonin da yan majalisun jiha

Abuja - Hukumar gudanar da zaben kasa ta INEC ta sanar da dakatar da zaben kujerar Sanata na mazabar Enugu ta yamma da aka shirya yi gobe, Asabar, 25 ga Febrairu, 2023.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya bayyana hakan a hira da manema labarai da yayi a birnin tarayya Abuja da ranar Juma'a, rahoton ChannelsTV.

Ya ce an dage zaben ne biyo bayan kisan dan takarar kujerar na jam'iyyar Labour Party LP.

INEC Chairam
Shugaban Hukumar INEC ya Dakatar Da Zaben Gobe
Asali: Original

Yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Kai Farmaki Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe A Bauchi

"Mun samu labari a hukumance daga wajen jam'iyyar tana mai sanar da INEC mutuwar dan takararta na mazabar Enugu ta gabas.
Jam'iyyar kuwa ta bayyana niyyar maye gurbin dan takararta da ya mutu. Wanda kuma daidai ne da doka.
Saboda haka hukumar ta dakatar da zaben mazabar kamar yadda doka ta tana. Babu zaben Sanata a mazabar Enugu ta gabas mai dauke da kananan hukumomi 6.
Yanzu za'a hada zaben da na gwamnoni da yan majalisar dokokin jiha da za'ayi nan da makonni 2 ranar 11 ga Maris, 2023.

Farfesa Mahmoud ya ce yanzu za'a yi zaben bayan makonni biyu tare da zaben gwamnoni da yan majalisar dokokin jiha.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida