"Ku Amince da Zabin Yan Najeriya" Shugaba Buhari Ya Fada Wa Yan Takara
- Shugaba Buhari ya bukaci masu takara a zaɓen 2023 su girmama kuma su aminta da zabin yan Najeriya
- Shugaban ya bayyana haka ne a wurin taron sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a Abuja ranar Laraba
- A cewarsa tun farkon zuwan gwaamnatinsa ta fara kokarin yadda zata gudanar da sahihin zabe
Abuja - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya shawarci yan takarar da zasu fafata a zabe mai zuwa a dukkan matakai da su aminta da zabin masu kaɗa kuri'a, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Buhari ya faɗi haka ne ranar Laraba a wurin taron rattaɓa hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya na masu neman zama shugaban kasa da shugabannin jam'iyyu 18.
Shugaban kasan ya ce tun farkon zuwan gwamnatinsa ta fara shirin yadda zata bar tarihin da za'a riƙa tunawa na, "Gudanar sahihi kuma amintacce zaɓe cikin zaman lafiya."
"Ina rokon 'yan takara na kowane mataki a zaɓe mai zuwa su girmama zaɓi da kuma muryar yan Najeriya masu kaɗa kuri'a kuma ku amince da sakamakon da INEC zata sanar, hukumar da doka da ɗorawa alhaki."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Duk wanda sakamakon bai masa daɗi ba yana da ikon kai ƙara Kotu, ya zama dole mu aminta da bangaren shari'a. Ina kara kira ga dukkan yan takara su cika abinda ke cikin yarjejeniyar da suka rattaɓa hannu yau."
Buhari ya kuma yaba wa kwamitim zaman lafiya na kasa (NPC), wanda a cewarsa duk da babu wani tallafin kuɗi da yake samu amma ya jajirce.
Ya ce ya samu masaniya kan damuwar da ake hasashe game da gudanar zaɓe mai zuwa da kuma abinda ka iya zuwa ya dawo bayan bayyana sakamako.
Daily Trust ta rahoto shugaban na cewa:
"Tun da na shiga Ofis, gwamnatina ba ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da ta bar tarihin gudanar da sahihin zaɓe. Zamu ci gaba da aiki a tsakiya kuma zamu bar doka ta yi aikinta kan duk abinda ya shafi siyasa."
Atiku Ya Kara Caccakar Gwamna Wike, Ya Ce Gwamnan Ba Zai Iya Baiwa Tinubu Kuri'un Ribas Ba
A wani labarin kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP ya ce gwamna Wike ba zai iya kawo wa Tinubu kuri'un jihar Ribas ba
Da yake maida masa martani, tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ce Wike ba zai iya fitowa fili ya faɗawa mutanen Ribas su dangwalawa APC ba.
Asali: Legit.ng