Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Ƴar Takarar Gwamnan Jihar Adamawa
- An dakatar da ƴar takarar gwamna mace ɗaya tilo a zaɓen gwamnan dake tafe a Najeriya
- Jam'iyyar APC a jihar Adamawa ta dakatar da ƴar takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar ta
- An dakatar da Aisha Binani ne dai bayan zarge-zargen da ake mata sun yi yawa sosai
Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa, ya dakatar da ƴar takarar gwamnan jihar.
Kwamitin ya dakatar da Aisha Binani, ƴar takarar gwamna a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar har na tsawon wata shida. Rahoton Ait.live
A wata takarda wacce mambobi 21 na kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙaramar hukumar suka rattaɓawa hannu, an zargi Binani da rashin bayyana a gaban wani kwamiti da aka kafa domin amsa tambayoyi kan laifukan da ake tuhumar ta da su na rashin ɗa'a.
Dakatarwar da aka yiwa Aisha Binani ta kawo ruɗani a cikin jam'iyyar APC a jihar Adamawa. Rahoton Leadership
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin ƙarar, an tuhumi Binani da tsoma baki wajen kawo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƴaƴan jam'iyyar tun bayan da ta lashe zaɓen fidda gwani.
Ana zargin ta da marawa wani ɓangare ɗaya kawai na jam'iyyar maimakon ace tayi ƙoƙarin yayyafawa rigimar cikin gida ta jam'iyyar ruwan sanyi.
Ana kuma zargn ta da rashin girmama ƙusoshin jam'iyyar wanda hakan ya sanya da yawan su suka fice suka koma wasu jam'iyyun adawa.
Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Tafi Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne
A wani labarin na daban kuma, wani na kusa da shugaba Buhari ya zolayi gwamnan Kano kan taƙaddamar tsofaffin takardun kuɗi na naira.
Bashir Ahmad, mashawarci na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan sadarwa na zamani, ya bukaci Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kai tsofaffin takardun nairansa babban bankin kasa, CBN, idan na halas ne.
Bashir Ahmad yayi raddi ne kan Ganduje bisa sukar sauya fasalin takardun naira da ya yi na cewa wani mataki ne kawo matsala ga demokradiyya da katsalandan ga babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng