Yan Daba Sun Farmaki Magoya Bayan Peter Obi a Legas, Sun Yi Barna
- Yan daba sun kaiwa ayarin magoya bayan Peter Obi hari a jihar Legas yayin da suke hanyar zuwa filin ralin LP
- Rahotanni sun nuna cewa maharan sun lalata motocin 'yan Obidient yayin harin na ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu
- Mutanen da harin ya shafa sun ce hakan ba zai sa su ja da baya ba kuma sun zargi APC da hannu a lamarin
Lagos - Wasu 'yan daba sun farmaki magoya bayan Peter Obi da aka fi sani da Obidient a yankin Lekki yayin da suke kan hanyar zuwa wurin kamfen shugaban ƙasa a jihar Legas.
Hakan na kunshe ne a wani sako da kakakin kwamitin kamfen Obi/Datti, Tanko Yunusa, ya aike wa wakilin jaridar Punch ranar Asabar 11 ga watan Fabrairu, 2023.
Ya ce:
"An kaiwa tawagar 'yan Obidient hari a Legas, sun hana mutanen mu zuwa wurin da aka shirya Rali. Ba abinda zai iya dakatar da mai lokaci. Hukumomin tsaro ya kamata ku san wannan."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Maharan sun tafka ɓarna
Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa maharan sun lalata Motoci da dama da suka kunshi ƙananan motoci na hawa da Bas da kuma Fasta mai ɗauke da Hoton Obi da Datti Bab Ahmed.
Bayanai sun nuna cewa magoya bayan na kan hanyar zuwa filiin wasan Tafawa Balewa Square domin halartar ralin jam'iyyar Labour Party, ba zato aka kai masu hari.
Hotuna da Bidiyoyi da aka wallafa a dandalin sada zumunta sun nuna irin ɓarnar da 'yan daban suka tafƙa yayin harin yayin da waɗanda suka jikkaya suka ɗora laifi kan APC.
Wa ke da hannu a kai harin?
Ɗaya daga cikin magoya bayan Obi da abun ya rutsa da su ya ce:
"Kaɗan kenan daga cikin abinda ya faru damu a hanyar zuwa wurin Rali. Zaka iya hasaso irin harin da aka kaiwa Bas din mu, 'yan Obidient da yawa sun jikka."
Wani ɗan Obidient ya ce yan daban sun tarwatsa su sun lalata masu abin hawa, ya kuma jaddada cewa ba zasu taba ja da baya ba.
Yace, "Ba zamu ja baya ba, ba zamu tsorata ba, duba abinda APC ta mana, sun kai mana hari a Jakande Roundabout, sun kwace mana komai."
A wani labarin kuma Mambobin APC a Jihar Ebonyi Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP Mako 2 gabanin zaɓe
Ɗan takarar gwamnan Ebonyi a inuwar PDP, wanda ya karbi masu sauya shekar ya ce lokaci ya yi da jam'iyyar zata koma kan madafun iko.
Masu sauya sheƙar sun ce sun yanke shiga PDP ne domin ba da gudummuwa wajen ceto Ebonyi da Najeriya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng