Kai Tsaye: Yadda Taron Kamfen Atiku da PDP Ke Gudana Yau A Kanon Dabo
Jirgin yakin neman zaben takarar kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 na jam'iyyar PDP ya dira jiha mai tarihi ta Kano a yau Alhamis, 9 ga watan Febrairu, 2023.
Hotuna daga filin kamfen yau

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Twitter

Asali: Facebook
Atiku ya shiga filin kamfe
Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan PDP sun dira filin taro.
Dubannan jama'a sun tarbe su yayinda suka isa.
Atiku ya kai gaisuwar ban girma fadar Sarkin Kano
Atiku Abubakar ya kai ziyarar ban girma fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.
Atiku ya jinjinawa Sarkin bisa dattakunsa.
A cewarsa:
"Mai martaba Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano, sarki ne na kirki a koda yaushe. Ko yanzu ya sake nuna hakan a ziyarar ban girman da na kai masa gabanin taron kamfenmu a jiha mai tarihi ta Kano."
Atiku ya kaddamar da makarantar da Malam Ibrahim Shekarau ya gina
Dirarsa Kano ke da wuya, Alhaji Atiku Abubakar, ya kaddamar da katafariyar makarantar da Sanata Ibrahim Shekarau, ya gina a jihar Kano.
Malam Ibrahim shekarau ya gina makarantar haddar Al-Qur'ani mai girma wacce aka yiwa suna, Kwaljin Al-Qur;anin tunawa da Gwani Muhammadu Dan Gunduwawa.
Atiku, shugaban PDP, Tambuwal, sun dira Kano
Dan takaran shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar; mataimakinsa, Ifeanyi Okowa shugaban uwar jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, da sauran jiga jiga jam'iyyar sun dira Kanon Dabo.