'Yan Daban PDP Sun Yi Garkuwa da Dan Takarar Gwamnan APC a Ribas
- 'Yan daban siyasa da ake kyautata zaton 'yan jam'iyyar PDP ne sun tsare dan takarar gwamnan APC a jihar Ribas, Tonye Cole
- Wannan shi ne karo ma biyu da tsagerun 'yan daba suka kai farmaki wurin da aka shirya Ralin kamfe cikin kwana 14 da suka shige
- Hukumar yan sandan jihar ba ta ce uffan ba kan lamarin amma ta tabbatar da harin da aka kaiwa ɗan takarar SDP
Rivers - Wssu yan daba da ake zargin na jam'iyyar PDP ne sun tsare ɗan takarar gwamnan APC a jihar Ribas, Tonye Cole, da sunan garkuwa da shi a garin Opobo.
A wani bidiyo da wani ganau ya tura wa wakilin jaridar The Nation, an ji karar harbe-harben bindiga kan mai uwa da wabi a garin.
Garin Opobo, nan ne mahaifar ɗan takarar gwamnan jihar Ribas a inuwar jam'iyyar PDP, Siminilayi Fubara.
Wannan shi ne karo na biyu da aka kai farmaki wurin ralin yakin neman zabe cikin mako biyu da suka shuɗe a jihar Ribas.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Harin farkon an kai shi ne a yankin birnin Patakwal, inda wani abun fashewa da ake zaton nakiya ce ya tashi da mutane, akalla mahalarta wurin 5 ne suka jikkata, rahoton Punch ya tabbatar.
Har yanzu rundunar yan sanda reshen jihar Ribas ba tace komai ba game da sabon harin da 'yan daban suka kai.
Yan bindiga sun farmaki tawagar SDP
Amma hukumar yan sandan ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun farmaki ɗan takarar gwamna a inuwar SDP, Sanata Magnus Abe, yayin da yake hanyar zuwa garin Akinima yin kamfe.
Mai magana da yawun hukumar reshen jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, tace jami'an tsaron da ke tare da tawagar Sanata Abe sun yi nasarar dakile harin wanda ya auku ranar Litinin.
Iringe-Koko, a wata sanarwa da ta fitar jiya, tace nan take hukumar yan sanda ta ƙara aika karin Dakarun sashin dabaru zuwa wurin domin su kai ɗauki.
A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Farmaki Ofishin INEC da Caji Ofis, Sun Halaka Mutum 1
'Yan bindiga sun tarwatsa ofishin 'yan sandan da na INEC a jihar Anambra ta hanyar jefa abubuwa masu fashewa gami da budewa jama'an yankin wuta.
Bayan haka an tattaro yadda 'yan bindigan suka bindige wata yarinya mai kimanin shekaru 15 a duniya yayin harin.
Asali: Legit.ng