Tsohon Gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow, Tare Da Mabiyansa Sun Fita Daga APC
- Jibrilla Umar Bindow ya sanar da fitarsa daga jam'iyya mai mulki a kasa watau jam'iyyar APC
- Bindow ya kasance gwamnan APC na farko a tarihin jihar Adamawa tun bayana kafa ta
- Tsohon gwamnan har yanzu bai bayyana inda ya nufa ba bayan fitarsa daga APC
Adamawa - Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Sanata Muhammad Umar Jibrilla Bindow, ya sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Bindow ya mulki jihar Adamawa tsakanin 2015 da 2019.
Ya aike wasikar fita daga APC ga shugaban jam'iyyar na gundumarsa ta Kolere, karamar hukumar Mubi ta Arewa ranar 20 ga Junairu, 2023, rahoton Leadership.
Dan siyasan dai har yanzu bai bayyana inda ya dosa ba amma ya ce dubunnan masoyansa zasu yi hijira da shi domin hada kan al'ummar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ya fita daga APC ne saboda rashin sulhun gaske tsakanin 'yayan jam'iyyar tun bayan shan kashin da yayi a zaben 2019 da kuma rikicin da ya biyo bayan zaben fidda gwanin 2022.
A cewar wasikar:
"Ina mai sanar da kai cewa nayi murabus matsayin mamban jam'iyyar All Progressive Congress party (APC) daga ranar 20 ga Junairu, 2023."
"Na yanke wannan shawara ne bayan addu'o'i da shawara da iyalaina, masu ruwa da tsaki da kuma mabiya a fadin jihar da kasa gaba daya."
"Na yi hakan ne bisa rashin jituwa da sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ta Adamawa tun bayan abinda ya faru a zaben 2019 da kuma bayan zaben 2022."
"Hakazalika ina sanar da kai cewa mabiyana na biye da ni wajen fita daga jam'iyyar don shiga sabuwar harkar hada kan al'ummar Adamawa."
Adamawa: Uwargidan Shugaban Kasa Zata Yi Sasanci Tsakanin Masu Rikici a APC
Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bayyana shirinta na shiga sasanci a rikicin jam’iyyar APC da yayi kamari a jihar Adamawa.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa, rikici ya harke a jam’iyyar APC reshen jihar bayan zaben fidda gwani na jihar wanda Sanata Aishatu Dahiru Binani, ta ci tare da lallasa Malam Nuhu Ribadu wanda yayi watsi da sakamakon tare da garzayawa kotu.
Babbar kotun tarayya dake zama a Yola a watan da ya gabata ta soke zaben fidda gwanin tare da bayyana cewa jam’iyyar bata da ‘dan takarar gwamna a zaben 2023 mai zuwa, lamarin da yasa APC tare da Binani da Ribadu suka garzaya kotun daukaka kara.
Asali: Legit.ng