Jama'ar Kano Ne sukace Nai Takara Ba Yin Kaina Bane Inji Dan Takarar Gwamnan Kano

Jama'ar Kano Ne sukace Nai Takara Ba Yin Kaina Bane Inji Dan Takarar Gwamnan Kano

  • Manyan Yan takarar shida ne ke fafatawa a kan kujerar gwamnan jihar Kano, ciki harda Mallam Ibrahim Khalil
  • A muhawarar da sashin hausa na BBC Hausa ya shirya ba'aga Mallam Ibrahim Khali a cikin jerin yan takarar ba
  • Mallam ibrahim khalil ya ajiye mai bawa gwamna shawara a karshen shekarar 2019 a gwamnatin ganduje

Kano - Kafar yada bayanai ta BBC ta yi hira da Mallam Ibrahim Khalil na jam'iyyar ADC, kan manufofinsa ga al'ummar Kano.

Mallam Ibrahim Khalil wanda yake malamin musulunci ne kuma haifaffen jihar kano.

A hirar da yayi da BBC Hausa Mallam Ibrahim Khalil ya fara da cewa:

"Ita wannan takarar da na ke a jam'iyyar ADC mai alamar musabaha, mutane ne suka ce azo ayi ba yin kaina bane"

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Bayan Sarkin Musulmi Ya Saka Baki, Yan Takarar Gwamna Na NNPP Da SDP Sun Janye Wa APC A Nasarawa

"Suna ganin duk cikin yan takarar nine zan iya tabbatr da adalci, dan haka suka dauko ni suka ce nazo nayi takara.

Mallam Ibrahim Khalil na cikin manyan yan takarar shida da zasu fafata a zaben gwamnan jihar kano da za'ai a watan maris din wannan shekarar da muke ciki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ibrahim Khalil
Jama'ar Kano Ne sukace Nai Takara Ba Yin Kaina Bane Inji Dan Takarar Gwamnan Kano Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Akwai Dr Nasiru Yusuf gawuna na jam'iyyar APC, da kuma Muhammad Abacha na jam'iyyar PDP, da kuma Salihu Tanko yakasai na jam'iyyar PRP.

Sauran sun hada da Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP, da Sha'aban Sharada na jam'iyyar ADP, da Bala Gwagwarwa na jam'iyyar SDP sai kuma mallam Ibrahim Khalil na jam'iyyar ADC

Manufofin mallam Ibrahim Khalil

Kafar BBC Hausa ta shirya muhawarar yan takarar gwamna a ranar 14 ga wannan watan da muke ciki, to sai da ba mallam ibrahim din a cikin wanda sukai muhawarar.

Kara karanta wannan

Ana Daf Da Zabe, Makisa Sun Kai Wa Dan Takarar Gwamnan PDP Hari

Muhawarar dai an shirya tane dan jin ta bakin yan takarar da kuma abinda suka shirya mutanen kano.

Mallam Ibrahim Khalil yace manufofinsa guda biyar ne, wanda suka hada da

1. Tabbatar da doka da oda

2. Muhalli

3. Lafiya

4. Ilimi

5. Tattalin arziki

Duk wadannan abubuwan da lissafa muku ina tabbacin cewa zan yi su, amma akwai wadanda idan suka fada basa yi.

Mallam Ibrahim Khalil yace:

"Ni duk wadannan jam'iyyun bana shayinsu, sabida ina da manufa mai kyau, kuma ina da tunani da niyya main kyau"
"Duk wadannan jam'iyyu jam''iyyu da aka gaji da su, sai dai sabbi da ga cikinsu wanda ba'asan yadda halinsu yake ciki ba

Zaku iya kallon bidiyon a kasa:

Batun yakin neman zabe

Mallam ibrahim khalil yace yadda yake yakin neman zabensa shine a kowacce rana yana zuwa karamar hukuma daya, sannan kuma mutane 20 ne kai suke binsa

Amma daga baya sun kara yawan masu bin nasa kamfe din zuwa mutum 50, sabida yadda mutane suke son su zo kamfe din.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida