APC A Jihar Plateau Tayi Babban Kamu, 'Dan Mantu Da Mutum 20,000 Sun Sauye Sheka Daga PDP
- Jam'iyyar PDP a jihar Plateau ce ta yi rashin dubban magoya bayanta a wannan marar ta neman magoya baya.
- 'Yan siyasa na sauyin sheka a wannan lokacin domin komawa ga inda suke ganin shine mafi dacewa a garesu
- Jam'iyyar APC dai ita ce ke mulki a jihar Plateau, sai jam'iyyar PDP mai adawa da ta ke da 'yan majalissun jiha, tarayya da kuma wasu masu fada aji a jam'iyyar
Plateau - Jam'iyyar APC rashen jihar Plateau ta yi babban kamu, inda ta samu dubban magoya baya da kuma wani jigo a jam'iyyar.
Umar Mantu lauya kuma 'da ga tsohon shugaban majalissar dattijai ta tarayya marigayi Sanata Ibrahim Mantu ya bar jam'iyyar PDP tare da koma jam'iyya APC tare da magoya bayansa wanda adadinsu zai kai mutum 20,000.
Sakataren yada labarai na jam'iyyar APC din jihar Sylvanus Namang ne ya tabattar da kowamar Mantun a wata sanarwa da ya fitar. Kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.
Bikin tabar Manto din dai ya gudana ne a gundumar Chanso da take karamar hukumar mulki ta Mangu a jihar.
Mantu dai yayi takarar fidda gwani ta dan majalissar tarayya sau biyu a mazabar Mangu/Bokkos ta jihar Plateau.
Jaridar Voiceofthepeople ta rawaito mantu matashi ne mai tarin goyan bayan matasa daga yankin da ya fito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani Babban Kusa A Jam’iyyar PDP ya Sauya Sheka Zuwa jam’iyyar APC Jihar Sokoto
Wani babban kujsa a jam'iyyar PDP a jihar sokoto, Alhaji Yusha'u Kebbe ya bayyyana sauya shekarsa daga jam’iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar Sokoto da tsohon gwamnan jihar Alu ke mata jagoranci.
Kebbe ya sanar da hakan ne a yayin da wata ganawa da yan jarida a Sokoto inda ya alakanta wannan matakin da ya dauka kan rashin jagoranci na gari da kasa samar da ababen more rayuwa da jam'iyyar PDP ta gaza yi a jihar.
Ya bayyana cewa da ya tuntubi magoya bayansa a dukkan kananan hukumomi 23 na jihar kafin yanke wannan hukuncin na na sauya sheka zuwa jam'iyyar APC in ji jaridar Vanguard
Asali: Legit.ng