Rikicin PDP: Gwamnonin G5 Sun Yanke Shawarar Wanda ZaSu Goyi Baya a 2023
- Tsagin gwamna Wike da ake kira G5 sun gaza yanke shawara bayan raba gari da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP
- Abinda ake sauraren ji shi ne wane ɗan takarar zasu dauka a matsayin shugaban kasa duk da sun ce ba zasu bar PDP ba
- Wata majiya tace kai ya fara rabuwa kan wanda ya dace su marawa baya tsakanin Peter Obi da Bola Tinubu
Ga dukkan alamu tsagin G5 na jam'iyyar PDP basu yanke ɗan takarar da zasu marawa baya a zaben shugaban kasa dake tafe a watan Fabrairu, 2023 ba.
Gwamnonin tawagar G5 sun ƙunshi, Nyesom Wike (Ribas), Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benue), Ifeanyi Ugwuayi (Enugu) da Okezie Ikpeazu (Abia).
Tawagar ta yi hannun riga mai neman zama shugaban kasa, Atiku Abubakar, saboda shugaban PDP na ƙasa ya ƙi sauka daga kujerarsa duk da ya yi alƙawarin hakan idan ɗan arewa ya ci zaɓen fidda gwani.
Wata majiya mai kusanci da G5 ta shaida wa The Nation cewa ra'ayin gwamnonin ya banbanta kan ɗan takarar zasu kulla alaƙa da shi bayan raba gari da Atiku.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shin batun sulhu a PDP ya sha ruwa kenan?
Mambobin G5 sun fahimci cewa babu sauran burbushin alamun za'a iya sulhu da Atiku Abubakar nan gaba ko tallata burinsa na zama shugaban kasa a 2023.
Wata majiya tace shugabancin PDP sun gaza nuna wata kwakkwarar alamar suna shirin shawo kan tawagar G5 da sauran masu ruwa da tsakin da aka ɓata masu gabanin 2023.
"Banga alamar sulhu ba ze yuwu ba kuma hakan ne abinda ke ran tsagin tawagar G5. Ɗan takara da shugabancin PDP ba su nuna alama zasu yi abinda muke so ba na sauya fasalin jam'iyya."
"Maimakon haka, suna ganin zasu ci zaɓen shugaban ƙasa ba tare da mu ba, taya mutanen da cewa sun son sulhi kuma za'a ji su suna ɓaɓatun zasu iya? Bukatar G5 ba ta ƙashin kansu bane amma sun ƙi ganewa."
- ini wata majiya a cikin G5
Wane ɗan takara gwamnonin zasu goyi baya?
Wata majiya ingantacciya ta ce gwamnonin G5 sun rabu kan wanda ya kamata su ɗauka tsakanin Peter Obi da Bola Tinubu.
Wasu daga cikin majiyoyin sun nuna cewa duk da sai an zauna sannan za'a yanke, tuni masu goyon bayan kowane ɓangare suka fara aiki ta karkashin kasa.
Ɗaya daga cikin majiyoyon ta ce:
"Har yanzun bamu zauna kan lamarin ba, amma a zahiri ba zamu goyi bayan Atiku ba amma tunda manyan mu sun amince su bayyana wa duniya inda muka dosa, zamu zauna mai yuwuwa a farkon 2023."
"A yanzu da nake magana masu son a dauki Obi da Tinubu na kokarin samun magoya baya gabanin taron. Har gwamnonin G5 suna da zaɓi, wasu na son Obi wasu kuma Tinubu."
A wani labarin kuma Gwamna Wike yace a watan Janairu mai zuwa zai bayyana wa duniya wnada zai wa kamfe a zaben 2023
A ranar Alhamis 22 ga watan Disamba, 2022, Gwamna Wike dake takun saka da Atiku Abubakqr, yace zai tallata ɗan takarar da ya zaɓa a dukkan sassan ƙasar nan.
Asali: Legit.ng