Nnamdi Kanu, Shugaban 'Yan Awaren IPOB na Bukatar Aiki a Zuciya

Nnamdi Kanu, Shugaban 'Yan Awaren IPOB na Bukatar Aiki a Zuciya

  • Lauya mai kare shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, Aloy Ejimakor, ya sanar da cewa Kanu yana dauke da ciwon zuciya
  • A cewar lauyan, wani asibiti ya bukaci yi wa Kanu aikin zuciya tun a watan Agusta da ya gabata amma gwamnatin tarayya bata sake shi
  • A takardar da ta bayyana daga asibitin, za a canzawa Kanu wani bawul ne a zuciyarsa kuma ciwon mai barazana ne ga rayuwarsa

FCT, Abuja - Aloy Ejimakor, lauyan shugaban 'yan awaren IPOB, Nnamdi Kanu, a ranar Asabar yace wanda yake karewa yana bukatar aiki a zuciya don canza masa wani bawul.

Yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta sako garkamammen shugaban 'yan awaren don ya samu taimako masana kiwon laifiya.

Mazi Nnamdi Kanu
Nnamdi Kanu, Shugaban 'Yan Awaren IPOB na Bukatar Aiki a Zuciya. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ejimakor ya wallafa shawarin da suka samu daga Pink Rose Hospital Limited a ranar 23 ga watan Agustan 2022 a shafinsa na Twitter kan cewa matsalar Kanu da ta danganci zuciya mai barazana ce ga rayuwa.

Kara karanta wannan

Bukola Saraki Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Kan Batun Gwamnan CBN

"Mara lafiyan yana bukatar aiki da gaggawa na zuciya domin sauya masa wani bawul."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Wani sashi na shawarar yace.

Ejimakor yace:

"Domin gujewa wata tantama, gwamnatin Najeriya ta san cewa tun a watan Agusta ya kamata a yi wa Mazi Nnamdi Kanu aiki.
"Baya ga umarnin kotu, wannan kadai ya isa yasa a sake shi ko a bashi damar samun taimakon asibiti. Wannan al'ada ce ta duniya."

An gurfanar da Kanu a ranar 19 ga watan Janairu a gaban Mai Shari'a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya dake Abuja.

Ya musanta aikata laifuka 15 da ake zarginsa da su da suka hada da ta'addanci.

Ya shigar da sukar laifukan inda ya roki kotun da ta yi watsi da su wanda kotun daukaka kara ta aminta da hakan.

A wannan ranar, wata babbar kotun Umuahia dake jihar Abia ta bukaci a biya Kanu diyyar N1 biliyan a hukuncin da ta yanke na hakkinsa na aka take, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN Ba Shi da Lafiya

Kotun daukaka kara ta sallami Kanu

A wani labari na daban, wata kotun daukaka kara dake zama a babban birnin tarayya na Abuja ta sanar da sallamar shugaban kungiyar 'yan aware ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Alkalai uku da suka jagoranci shari'ar a kotun sun yi watsi da zargin ta'adda tare da cin amanar Najeriya da ake zarginsa da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel