Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
- Shugaban majalisar dokokin jihar Taraba, Farfesa Joseph Albasu Kunini, ya yi murabus daga kujerarsa ranar Laraba, 21 ga watan Disamba
- Mataimakin kakakin majalisar, Hamman Adama Ibn-Abdullahi, ne ya karanta wasikar murabus din, sai dai yace ya yi haka bisa kashin kansa
- A zaman wanda aka fara tun kafin lokacin da aka saba, mambobin majalisar sun amince da zaben John Kizito Bonzena a matsayin sabon shugabansu
Taraba - Kakakin majalisar dokokin jihar Taraba dake arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Joseph Albasu Kunini, ya yi murabus daga kujerasa kan dalilan kai da kai, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Farfesa Kunini ya sanar da matakin murabus ɗin ne a wata wasika da ya aike wa mambobin majalisar ranar Laraba, 21 ga watan Disamba, 2022.
Mataimakin kakakin majalisar, Hamman Adama Ibn-Abdullahi, wanda ya jagorancin zaman na gaggawa ne ya karanta takardar nurabus ɗin tsohon kakaki ga zauren.
Jaridar Punch ta tattaro cewa Farfesa Joseph Kunini, ya rike mukamin shugaban majalisar dokokin Taraba tun watan Disamba, 2019 har zuwa yau Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karo na karshe da tsohon kakakin ya yi aiki shi ne ranar Litinin ɗin da ta gabata lokacin da ya miƙa wa gwamna Darius Ishaku kundin kasafin kuɗin 2023 domin ya zartar da shi.
Shugaban masu ladaftarwa na majalisar, John Kizito Bonzena, wanda ke wakiltar mazaɓar Zing, shi ne mambobin majalisar suka zaɓa a matsayin sabon shugaba ba tare da gardama ba.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a yau da kullum majalisar ta saba fara zama da misalin ƙarfe 10:00 na safe, amma zaman Laraba wanda tsohon kakaki ya yi murabus an fara shi tun kafin wannan lokaci.
John Kizito Bonzena, mamban jam'iyyar PDP ne ya zama sabon shugaba a zaman kuma har yanzun babu wani sahihin bayani kan juyin siyasar da ta yi gaba da kujerar kakakin.
Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Kakakin Majalisar Wakilai Kan Muhimman Abu 2
A wani labarin kuma Shugaban Kasa Buhari ya gana da kakakin majalisar dokokin tarayya, Femi Gbajabiamila a Abuja
Ganawar shugabannin biyu ta maida hankali ne kan sabon tsarin da babban bankin Najeriya (CBN) ya ɓullo da shi na kayyade yawon kuɗi a hannu.
Shugaban majalisar yace sun kuma taɓo wasu batutuwa da suka shafi babban zaben 2023 da ke tafe nan da watanni biyu.
Asali: Legit.ng