Yadda Jihar Kaduna Ta Cika Ta Batse Jiya Don Taron Kamfen APC
Tawagar yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyya mai gwamnati ta All Progressives Congress APC, ya yada zango jihar Kaduna, Arewa maso yammacin Najeriya Jiya Talata, 13 ga watan Disamba.
Kaduna garin Gwamna ta cika ya banbatse jiya da manyan jigogin jam'iyyar APC.
Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 na APC, ya isa Kaduna ne tare mataimakinsa, Kashim Shettima da Shugaban uwar jam'iyyar, Abdullahi Adamu.
Bayan taron, Kashim Shettima ya fitar da jawabin godiya ga al'ummar Kaduna bisa kyakkyawan tarbar aka yi musu
Yace:
"Mungode Kaduna"
Kalli hotunan taron:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Asiwaju Bola Tinubu Ya Dira Kaduna Yakin Neman Zabe, Ya Garzaya Birnin Gwari
Mai neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya dira jihar Kaduna don kaddamar da yakin neman zaben yankin Arewa maso yamma.
Tinubu ya isa Kaduna ne ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, 2022.
Dan takaran ya samu rakiyar abokin tafiyarsa, Sanata Kashim Shettima; Dirakta Janar na kamfen kuma gwamnan Plateau, Simon Lalong; Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, tare da dan takaran gwamnan APC na jihar, Sanata Uba Sani suka tarbesu a filin tashin jirgin saman jihar.
Tinubu ya tafi gari mai hadari, Birnin Gwari
Dirarsa ke da wuya, tsohon gwamnan na Legas ya garzaya karamar hukumar Birnin Gwari, daya daga cikin garuruwan da yan bindiga suka addaba a jihar.
Ya tafi ziyartar iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Ya samu rakiyar Gwamna Nasir El-Rufa'i, Sanata Uba Sani, da sauran mambobin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng