Shugaban Jam'iyyar PDP a Kaduna Ta Tsakiya Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaban Jam'iyyar PDP a Kaduna Ta Tsakiya Ya Rigamu Gidan Gaskiya

  • Shugaban PDP a shiyyar Kaduna ta tsakiya, Shehu Ahmed Giant, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar Talatan nan 13 ga watan Disamba, 2022
  • A wata sanarwa da Usman Muhammad Gwarzo ya fitar yace marigayin, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa ya rasu ne a Asibitin 44
  • Ya kuma bayyana cewa an shirya za'a masa Sallar jana'iza a Masallacin Sultan Bello bayan sallar Azuhur yau Talata

Kaduna - Da safiyar Talatan nan 13 ga watan Disamba, 2022 muka samu labarin rasuwar shugaban jam'iyyar PDP na shiyyar Kaduna ta tsakiya, Shehu Ahmad Giant.

Marigayi Shehu Giant, tsohon shugabar ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa, ya ce ga garinku nan ne a Asibitin Sojojin Najeriya na 44 dake cikin birnin Kaduna.

Shehu Ahmed Giant.
Shugaban Jam'iyyar PDP a Kaduna Ta Tsakiya Ya Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: aminiya
Asali: UGC

Jaridar Aminiya Daily Trust tace Usman Muhammad Gwarzo ne ya sanar da rasuwar Shehu Giant da safiyar Talata.

Kara karanta wannan

Hotunan Yadda Yakin Neman Zaben Atiku/Okowa Ya Gudana Yau A Jihar Nasarawa

Sanarwan tace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kowane mai rai mamaci ne, Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un, ba da jimawa ba Honorabul Shehu Ahmad Giant, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa kuma shugaban PDP na shiyyar Kaduna ta stakiya ya rasu."

Sanarwan ta ƙara da cewa za'a yi wa marigayin gata na karshe watau Sallar Janaza da kuma kai shi makwancinsa bayan Sallar Azahar a Masallacin Sultan Bello yau.

Sanarwan ta ci gaba da cewa:

"Muna Addu'a Allah SWT ya sa gidan Aljannatul Firdausi ya zame masa makoma ta karshe bayan rasuwarsa. Za'a yi jana'izarsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna bayan Sallar Azuhur."

Bayanai sun nuna cewa kafin rasuwar marigayi Shehu Ahmed Giant ya jima yana fara da rashin lafiya da ta kai ga kwantar da shi a Asibiti don zama karkashin kulawar Likitoci.

Zaben 2023: Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Na PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kara karanta wannan

Tinubu Ko Atiku? Babban Malami Ya Fito Fili, Ya Faɗi Wanda Ba Abinda Zai Hana Shi Zama Shugaban Kasa a 2023

A wani labarin kuma kun ji cewa ɗan takarar majalisar tarayya daga jihar Osun karkashin inuwar PDP a 2023, Mista Sola Arabambi, ya kwanta dana

Wani makusancin ɗan siyasan wanda ya nemi a sakaya bayanansa yace Uban gidansa ya rasu ne ranar Asabar, 3 ga watan Disamba, 2022 bayan fama da rashin lafiya ta ƙankanin lokaci.

Tuni dai yan uwa da abokanan arziki da abokan siyasa suka fara tururuwar tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da jam'iyyar PDP baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262