2023: Zamu Yanke Dan Takarar Shugaban Kasa Da Mutanen Ribas Zasu Zaba, Wike

2023: Zamu Yanke Dan Takarar Shugaban Kasa Da Mutanen Ribas Zasu Zaba, Wike

  • Gwamnan jihar Ribas yace nan ba da jimawa ba zai bayyana ɗan takarar shugaban ƙasar da mutanensa zasu zaɓa a 2023
  • Nyesom Wike ya roki mazauna Ribas su goyi bayan yan takarar PDP a zaben gwamna da na yan majalisar tarayya da jiha
  • Jagoran G5 na takun saka da shugabancin PDP kuma ana fargabar hakan ka iya ja wa Atiku rashin nasara a 2023

Rivers - Gwamna Nyesom Wike yace jam'iyyar PDP a jihar Ribas zata bayyana wanda zata mara wa baya a zaɓen shugaban kasan 2023 da ke tafe.

Channels tv tace Wike ya faɗi haka ne yayin kaddamar da Titin Rukpokwu-Igwuruta a ƙaramar hukumar Obio-Akpor, jihar Ribas ranar Talata.

Gwamnan ya roki mutanen jihar Ribas su zaɓi PDP a zaben gwamna, majalisun tarayya, da na majalisar dokokin jiha a 2023.

Kara karanta wannan

2023: APC Ta Hargitse a Jihar Arewa Yayin da Wani Sanatan Jam'iyyar Ya Gana da Ɗan Takarar PDP

Gwamnan Ribas, Nyesom Wike.
2023: Zamu Yanke Dan Takarar Shugaban Kasa Da Mutanen Ribas Zasu Zaba, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Haka zalika gwamnan, jagoran tawagar G5, ya gaya wa mazauna jiharsa cewa nan ba da jimawa ba zasu yanke ɗan takarar da ya dace su goyi baya a zaɓen shugaban ƙasa na 25 ga watan Fabarairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Shin zaku zabi ɗan takarar gwamnan mu? Zaku zaɓi masu neman kujerar Sanatoci? Zaku zaɓi 'yan takarar majalisar wakilan tarayya? Zaku zaɓi 'yan takarar majalisar Dokoki?" Wike ya tambayi dandazon mutane suka ce "Eh."

"Ragowar ɗayan kuma zan zo na faɗa muku wanda zaku baiwa kuri'unku. Ku kwantar da hankulanku zan faɗa muku karku damu amma waɗanda na ambata ku tabbata kun zaɓe su."
"Nan ba da jimawa ba zamu zauna mu yanke shawarar inda muka dosa (a zaɓen shugaban kasa)."

- Gwamna Wike.

Gwamna Wike, mamba a jam'iyyar PDP, ba ya ga maciji da ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa, Alhaji Atiku Abubakar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Mun Tafka Babban Kuskure, Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben Atiku Ya Magantu

Ya yi wa ɗan takara a inuwar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, da takwaransa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, alƙawarin taimaka musu da kyayyakin kamfe a Ribas.

Yayin da ya rage watanni uku gabanin zaɓen 2023, ana fargabar mai yuwuwa rigimar Wike kan bukatar sauya Ayu daga mukamin shugaban PDP ya shafi damar Atiku na cin zaɓe a 2023.

Shehu Sani Ya Tona Asirin Abinda Yasa Ake Kai Hari da Ƙona Ofisoshin INEC Gabanin 2023

A wani labarin kuma Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya yace masu kai hari Ofisoshin INEC burinsu su hana zaɓen 2023

Sanata Shehu Sani yace waɗannan hare-haren 'yan bindiga na kaisu ne da kona Ofisoshin da nufin zagon ƙasa ga shirin INEC ta gudanar da zabe.

A yan kwanakin nan, maharan sun kone ofishin INEC na ƙaramar hukumar Izzi a jihar Ebonyi, inda suka kone muhimman kayayyakin zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262