Jam’iyyar PRP Ta Karyata Batun Hadewa Da APC a Jihar Sakkwato

Jam’iyyar PRP Ta Karyata Batun Hadewa Da APC a Jihar Sakkwato

  • Jam'iyyar PRP a jihar Sakkwato ta yi martani ga rade-radin cewa ta rushe cikin jam'iyyar APC gabannin zaben 2023
  • PRP ta ce wannan yaudara ce kawai domin duk shugabanninta na nan baya ga dan takarar gwamna da wasu biyu da suka fice zuwa jam'iyya mai mulki
  • Sakataren jam'iyyar na kasa, Malam Ibrahim Tudun-Doki, ya ce ba za su hana kowa sauya sheka ba amma babu batun hadaka

Sokoto - Jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP) reshen Sakkwato ta karyata rade-radin da ake yi cewa ta hade da jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar, jaridar PM News ta rahoto.

Dan takarar gwamna na PRP a jihar, Alhaji Sa’idu Gumburawa, tare da sauran mambobin jam'iyyar sun sanar da sauya shekarsu daga jam'iyyar zuwa APC a hukumance a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Surukin Shugaba Buhari Ya Sauya Sheka Daga APC, Ya Fadi Dalili

Jam'iyyar PRP
Jam’iyyar PRP Ta Karyata Batun Hadewa Da APC a Jihar Sakkwato Hoto: PM News
Asali: UGC

Gumburawa, wanda ya samu tarba daga Sanata Aliyu Wamakko ya ce dukkanin yan takarar PRP da shugabannin jam'iyyar a matakin jiha da kananan hukumomi sun amince da shawarar jam'iyyar na komawa APC.

Jam'iyyar PRP na nan daram-dam bata rushe cikin APC ba

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a Sakkwato, Malam Ibrahim Tudun-Doki, babban sakataren PRP na kasa, ya ce jawabin abun takaici ne kuma yaudara ce tsantsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Jam'iyyar PRP a Sakkwato na nan daram-dam kuma mun ankara da hukucin da dan takarar gwamnan da wasu biyu suka dauka lokacin da muka ga rahoton a kafar sadarwa.
"Wannan ya yi sanadiyar da muka kira taron gaggawa na masu ruwa da tsaki a yau don bayyana matsayinmu game da ficewar dan takarar gwamnan.
"Kamar yadda kuka sani, muna a cikin tsarin damokradiyya ne wanda kowa ke da yancin kansa, don haka ba za mu hana kowa yancinsa ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Yi Murna Yayin da Kwankwaso Ya Yi Babban Rashi a NNPP

"Amma jam'iyyarmu na nan daram-dam a Sokoto, dukkanin shugabannin jam'iyyar na tare da PRP baya ga mataimakin shugaba da dan takarar sanata na Sakkwato ta gabas da suka bi sahun dan takarar gwamna.
"Saboda haka, muna masu sanar da mutanen kirki na jihar Sakkwato cewa PRP na nan daram-dam kuma za mu ci gaba da neman nasarar jam'iyyarmu."

Tudun-Doki, wanda ke neman takarar kujerar dan majalisar wakilai na PRP a mazabar Gwadabawa/Illela, ya ce jam'iyyar reshen jihar zata sanar da hedkwatarta ta kasa a hukumance don maye gurbin su, rahoton Vanguard.

2023: Tinubu da Shettima ba za su ci zabe ba, Babachir

A wani labarin, Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce Asiwaju Bola Tinubu ba zai ci zabe ba a 2023.

Lawal ya danganta hakan da zaban Kashim Shettima da dan takarar shugaban kasar na APC yayi, yana mai zargin cewa an mayar da kiristocin arewa saniyar ware.

Kara karanta wannan

'Dan Takarar Gwamna, 'Yan Takarar Majalisar Tarayya da Majalisar Jiha Sun Aje Tikitinsu, Sun Koma APC a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng