Ta karewa Atiku Da Obi Bayan Da Kashim Shattima Yai Hasashen Wanda Zai Ci Zaben 2023
- Dan takarar Mataimakin Shugaban kasa a APC ya bayyanawa ‘yan Najeriya wadanda za su kada kuri’a a zabe mai zuwa
- Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima a wani shiri a Abuja ya ci gaba da cewa bai kamata Atiku Abubakar da Peter Obi su tsaya takarar shugaban kasa a 2023 ba.
- A cewar tsohon gwamnan jihar Borno, ‘yan biyun na da aniyar sake mayar da kasar nan gaba ba tare da wani kyakkyawan shiri ga ‘yan Najeriya ba.
Abuja - Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ya ce ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, da takwaran sa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, ba su da wani abin da za su iya ga yan Najeriya.
Shettima ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Nuwamba a Abuja, yayin wani taron kwana guda kan shirin da suka yiwa Najeriya.
Zamu Kada Atiku da Obi A Zaben 2023, in ji Shettima
A rahoton Daily Trust, ya ce zaben shugaban kasa na 2023 zai zama Abin kwatance a tarihin Najeriya, yana mai cewa “Obi ba shi da wani abin da zai iya yi baya ga alkaluman da yake yawan furtawa na shaci-fadi."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shettima ya kuma ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ne zai kayar da Atiku da Obi, yana mai cewa Ya fi su tunani da basira.
Tarihi: Cikakken jerin sunayen 'yan takarar shugaban kasa da suka kauracewa muhawara
A ci gaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa a shekarar 2023, al’amura sun Nisa, kuma ana ci gaba da nuna damuwa a zukatan ‘yan kasar kan wanda zai zama shugaban kasar Najeriya.
Masana harkokin siyasa da dama sun bayyana zabukan da ke tafe a matsayin tseren dawakai uku domin kuwa babu Wani hasashe na waye shugaban kasa.
Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, da Peter Obi na jam’iyyar Labour ne manyan ‘yan takara uku da ke neman Shiga fadar Aso Rock, a cewar ra’ayin jama’a.
Babban daraktan Kwamittin yakin neman zaben Obi/Datti, Doyin Okupe, ya ce Peter Obi zai Zai Ringa Zuwa Muhawara ne da Takwarorinsa Ba Wakilai ’yan takarar shugaban kasa na wasu jam’iyyun siyasa ba.
Da yake magana a wani taron manema labarai da Legit.ng ta samu a Abuja, Okupe ya ce girman kan da ‘yan takarar shugaban kasa na wasu jam’iyyun siyasa ke nunawa a zaben 2023 abu ne da ba za a iya misaltawa ba.
A cikin jawabinsa, Okupe ya ce dole ne a aiwatar da shirin na sauya Najeriya da wani tsari na gari.
Asali: Legit.ng