Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Wakilai Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC

Shugaban Masu Rinjaye A Majalisar Wakilai Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC

  • Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, ya karyata rade-radin cewa yana shirin barin APC zuwa wata jam’iyya gabannin 2023
  • Doguwa ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, a Abuja a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba
  • Dan majalisar tarayyar ya ba Tinubu tabbacin samun goyon bayansa a 2023, yana mai cewa tsohon gwamnan na jihar Lagas na da karfi da tarin kwarewa don daidaita tattalin arzikin Najeriya

Abuja - Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya ce har yanzu shi dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne kuma bai da wani dalili na barin jam’iyyar imma a yanzu ko a nan gaba.

Ya ce wadanda ke zargin yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar suna yada labaran karya ne kawai.

Kara karanta wannan

Rikicin Afenifere: Kungiyar Yarbawa Ta Ragargaji Tinubu, Ta Masa Lakabi Da 'Babban Mai Raba Kawuna'

Doguwa da Tinubu
Shugaban Masu Rinjaye Doguwa Ya Magantu Game Da Batun Sauya Shekarsa Daga APC Hoto: Tunde Rahman
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Tunde Rahman, hadimin dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya aikewa Legit.ng a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba.

Legit.ng ta tattaro cewa Ado Doguwa, wanda ke wakiltan mazabar Doguwa/Tudun Wada ta jihar Kano a majalisar wakilai, ya magantu ne lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Tinubu a Abuja a ranar Lahadi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban masu rinjayen ya samu rakiyar dan majalisar jihar da ciyamomi biyu daga mazabarsa da kuma sauran manyan shugabanni daga jihar.

Zaben 2023: Doguwa ya baiwa Tinubu tabbacin samun goyon bayansa

Da yake ba Tinubu tabbacin samun goyon bayansa da kuma ci gaba da kasancewa a APC, ya ce gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje na a hannu nagari.

Tinubu ya yi godiya ga Tinubu

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Jigo Ya Gargadi Jam’iyya, Yace ‘Dan Takaran Kano Yana Tare da Atiku

Asiwaju Tinubu ya mika godiya ga Ado Doguwa kan wannan ziyara da ya kai masa, yana mai alkawarin kasancewa tare da shi da mutanen jihar kan goyon bayansu.

Ya tuna cewa sun dade da Ado Doguwa, daga zamaninsu a majalisar dokokin kasar a 1992, shi yana majalisar dattawa sannan Doguwa na a majalisar wakilai, inda ya bayyana shugaban masu rinjayen a matsayin dansa kuma na hannun damarsa.

2023: APC ta Tarbi Fiye Da Mutum 1000 Da Suka Sauya Sheka Daga PDP A Zamfara

A wani labarin, shugabar matan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, Hajiya Madina Shehu, ta sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

PM News ta rahoto cewa Madina Shehu ta sanar da sauya shekar tata ne a ranar Alhamis bayan wata ganawa da tayi da Gwamna Bello Matawalle a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.

Ta bayyana cewa bar PDP ne saboda rashin tsari na shugabanci a cikin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin APC 5 Na Tattaunawa da Atiku Abubakar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng