2023: APC Ta Yi Babban Kamu A Sokoto Yayin Da Dattijon Jigon PDP Da Mutanensa Suka Sauya Sheka
- Alhaji Sahabi Bojo-Bodinga, jigon jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ya fita daga jam'iyyar ya koma jam'iyyar APC
- Sanata Aliyu Wamakko, jagoran jam'iyyar APC a Sokoto ne ya tarbi shi a gidansa a ranar Juma'a 4 ga watan Nuwamba
- Alhaji Isa Sadiq-Achida, shugaban APC na Sokoto, ya yi maraba da Bojo-Bodinga ya kuma masa alkawarin za a masa adalci da mutanensa
Sokoto - Gabanin babban zaben shekarar 2023, daya cikin dattawan jiga-jigan yan jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, Alhaji Sahabi Bojo-Bodinga, ya koma APC, rahoton The Punch.
Jagoran APC a jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, ne ya tarbi Bojo-Bodinga, jigon PDP daga Sokoto South a gidansa a ranar Juma'a a Sokoto.
Hakan na cikin wata sanarwa da mashawarcin Wammako na musamman a sabuwar kafar watsa labarai, Bashar Abubakar ya rabawa manema labarai a Sokoto, ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar ya ce wadanda suka hallari taron sun hada da Ministan Harkokin Yan Sanda, Maigari Dingyadi' Dan takarar gwamna na APC a jihar, Alhaji Ahmad Aliyu; da manyan yan APC a jihar, PM News ta rahoto.
Ya ruwaito shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Isa Sadiq-Achida, a lokacin da yake magana a madadin jam’iyyar yana tabbatar wa sabon dan jam’iyyar da magoya bayansa cewa daidai suke sauran mambobin jam’iyyar.
Shigowar Bojo-Bodinga APC alheri ne, in ji Sadiq-Achida
Kalamansa:
"Wannan babban cigaba ne ga jam'iyyar mu kuma na tabbata da irin mutanen da ke APC ke cigaba da shigowa APC gabanin babban zabe, hakika Allah ya mana albarka.
"Na yi imanin shigowar Bojo-Bodinga, alheri ne ga APC kuma alama ce da ke nuna nasarar jam'iyyar a dukkan matakai."
A bangarensa, Bojo-Bodinga ya ce shi da magoya bayansa na PDP a fadin jihar sun bar jam'iyyar zuwa APC har abada.
Sokoto: Yadda Jam'iyyar PDP Tayi Babban Kamu, Dubban Mabiya APC sun Sauya Sheka
A kalla 'yan kasuwa 1,868 daga yankunan kasuwanci 10 na jihar Sokoto a ranar Laraba suka bar jam'iyyar APC tare da komawa jam'iyyar PDP.
Wadanda suka sauya shekar sun alakanta yin hakan da tsarin shugabanci nagari na Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal a matsayin daya daga cikin dalilan da yasa suka koma PDP.
Asali: Legit.ng