Idan Nayi Nasara, Zan Dora Daga Inda Ka Tsaya: Tinubu Ya Yiwa Alkawari Buhari

Idan Nayi Nasara, Zan Dora Daga Inda Ka Tsaya: Tinubu Ya Yiwa Alkawari Buhari

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawari cigaba da inda Buhari ya tsaya idan yayi nasa a 2023
  • Da Sannu Yan Najeriya Zasu Fahimci Irin Namijin Kokarin da Shugaba Buhari yayi, cewar Tinubu
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi dai ya cika alkawuran da ya yiwa al'ummar Najeriya

Abuja - Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressves Congress APC, Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa zai cigaba da ayyukan Shugaba Buhari idan yayi nasara a 2023.

Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da yayi na fatan alheri ga Buhari a taron bitar ayyukan Ministoci da Sakatarorin din-din-din dake gudana a Abuja, rahoton Channels.

Yace idan ya ci zabe, ba zai yi kasa gwiwa ba wajen ganin an tarwatsa yan ta'adda a Najeriya.

Kara karanta wannan

Cin Bashi Don Gudanar Ayyukan Cigaba Ba Laifi Bane: Cewar Bankin CBN

Ya yiwa Buhari alkawarin cewa zai karrama dukkan ayyukan da shugaban kasa yayi kuma ba zai watsa masa kasa a ido ba.

Ya kara da musamman zai kammala ayyukan gine-gine da gwamnatin Buhari ke yi.

Tinubu
Idan Nayi Nasara, Zan Dora Daga Inda Ka Tsaya: Tinubu Ya Yiwa Alkawari Buhari Hoto: BUhari
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

Bola Tinubu, a ranar Talata ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa kokarin da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Tinubu ya ce Buhari ya kwantar da hankalinsa, da sannu yan Najeriya zasu fahimci darajarsa.

Dan takaran yace ya kamata yan Najeriya su fahimci cewa Buhari ya tarar da matsalar tsaro da rashawa lokacin da ya karbi mulki daga wajen Jonathan.

An ruwaito Tinubu da cewa:

"A yanzu ba za'a yabawa kokari da wahalar da ya (Buhari) sha ba. Amma da sannu za'a fahimci irin namijin gudunmuwar da ya bada."

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

"Gwamnatin nan ta gaji matsaloli da dama. Daga baya ka (Buhari) fuskanci matsalolin da ba'a tsamanni kuma suka sake rikirkita lamura. Cutar Korona ta girgiza tattalin arzikin duninya, farashin danyen mai ya sauka hakazalika kudaden shiganmu."

Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron bita kan ayyukan da Ministocinsa sukayi cikin shekaru 7 da suka gabata tun da ya hau mulki.

Buhari ya bayyana cewa lallai ko shakka babu ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Taron ya samu halartan tsohon shugaban kasar Kenya, Uhurru Kenyatta, rahoton Leadership.

Shugaban kasan ya bayyana irin nasarorin da ya samu a bangaren aikin noma, gine-gine, tsaro, kiwon lafiya, yaki da rashawa, dss.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags: