Rikicin APC: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Makomar Takarar Sanata Ahmad Lawan a 2023
- Babbar Kotun tarayya dake Damaturu ta shirya gabatar da hukunci kan rikicin jam'iyyar APC a mazaɓar Sanatan Yobe ta arewa
- Bashir Machina, wanda ya lashe zaɓen fidda gwani a watan Mayu ne ya kai ƙarar domin neman hakkinsa da ake neman danne masa
- Jam'iyyar APC ta mika sunan shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ga INEC duk ba shi ya lashe zaɓe ba
Yobe - Babbar Kotun tarayya da ke zama a Damaturu, babban birnin jihar Yobe ta zaɓi ranar 28 ga watan Satumba, 2022 domin raba gardama tsakanin Bashir Machina da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.
Premium Times ta ruwaito cewa, Mista Machina ya garzaya Kotun Damaturu ne domin neman ta tilasta wa hukumar zaɓe INEC ta buga sunansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na takarar Sanatan Yobe ta arewa a inuwar APC.
Machina ya roki Kotun ta yi dokar da zata tilasta wa INEC karban sunansa a matsayin ɗan takarar APC bayan lashe zaben fidda gwani wanda ya gudana ranar 28 ga watan Mayu.
Haka zalika, ya nemi Kotun ta umarci jam'iyyarsa APC ta tura sunansa ga hukumar zabe mai zaman kanta kasancewar shi ya yi nasara a zaɓe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A ranar 12 ga watan Satumba, Alkalin dake jagorantar shari'ar, Mai Shari'a Fadima Aminu, ta ɗage yanke hukunci bayan lauyoyin kowane ɓangare sun gama gabatar da shaidunsu ga Kotu.
Mai Shari'ar ta bayyana cewa za'a sanar da ranar yanke hukunci a lokacin da ya dace ga kowane ɓangare.
Yaushe ne ranar yanke hukunci?
Legit.ng Hausa ta tabbatar da cewa Kotu zata bayyana hukuncin da ta yanke kan Kes ɗin a ranar Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ɗaya daga cikin lauyoyin da ke fafata shari'ar, wanda ya nemi kada a bayyana sunasa saboda ba shi da hurumin magana da yan jarida, ya tabbatar da sanya ranar.
Yayin da aka tuntube shi domin tabbatar lamarin, Hussaini Mohammed Isa, kakakin Mista Machina, ya amsa da cewa, "Eh ranar 28 ga watan Satumba, 2022 ce ranar yanke hukunci."
A wani labarin kuma Kwankwaso Ya Mamaye Mahaifar Shugaba Buhari, Ya Baiwa Mutane Mamaki
Mai neman kujerar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara jihar Katsina.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya buɗe sabuwar Sakatariyar jam'iyya mai kayan marmari a mahaifar shugaban ƙasa, Daura.
Asali: Legit.ng