2023: Dan Takarar Shugaban Kasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Gana da Gwamnan APC
- Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, na jam'iyyar APC ya ziyarci tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso
- Kwankwaso mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar NNPP yace ya karɓi bakuncin gwamnan ranar Laraba da daddare a Minna
- Wannan na zuwa ne yayin da ya rage 'yan watanni gabanin fayyace wanda zai gaji shugaban ƙasa Buhari a 2023
Minna, jihar Niger - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi baƙuncin gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a Minna.
A wani rubutu da ya saki da safiyar yau Alhamis a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita, Kwankwaso, yace ya gana da gwamnan na jam'iyyar APC ne jiya da daddare.
"A daren da ya gabata, na karɓi baƙuncin ɗan uwana, mai girma gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a masauki na dake Minna. Ina gode wa gwamna bisa wannan ziyara da karamcinsa," Inji Kwankwaso.
Tsohon gwamnan Kano ya ziyarci jihar Neja ne a cigaba da kokarin cika burinsa na zama shugaban ƙasa a Najeriya yayin da babban zaɓe ke tunkaro wa.
Hotunan ziyarar gwamnan Neja
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Babban zaɓen 2023
Ana ganin cewa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP na ɗaya daga cikin yan takarar dake sahun gaba a neman kujera lamba ɗaya a Najeriya a zaɓen 2023 dake tafe.
Tsohon gwamnan zai gwabza da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na PDP gabanin tantance wanda zai gaji Buhari.
Duk da raɗe-raɗin da mutane ke yaɗawa cewa ɗan takarar ka iya janye wa Atiku ko Tinubu, Kwankwaso yace ba gudu ba ja da baya, yana da goyon bayan al'umma kuma NNPP ke da nasara.
A wani labarin kuma Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Ya Fice Daga PDP, Yana Shirin Shiga jam'iyyar APC
2023: Ɗan Takarar Gwamna, Sakataren Jiha da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar PDP a Jihar Arewa
Alhaji Abba Gana Tata, ya sanar da jagororin PDP a jihar Yobe cewa daga ranar 13 ga Satumba, 2022, ya fice daga jam'iyyar baki ɗaya.
Sakataren PDP na jihar Yobe, da wasu shugabannin a mataki daban-daban sun bi sahun Abba Gana sun fice daga jam'iyyar.
Asali: Legit.ng