2023: Dole Ayu Ya Yi Murabus, Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga NEC

2023: Dole Ayu Ya Yi Murabus, Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga NEC

  • Duk da kaɗa kuri'ar amincewa da Ayu, Gwamnan Ribas ya jaddada matsayarsa cewa dole shugaban PDP ya yi murabus
  • Majalisar zartarwa ta jam'iyyar PDP ta kasa (NEC) ta tabbatar da cewa Ayu zai cigaba da jan ragamar jam'iyya a taron yau a Abuja
  • Gwamnan Wike yace ya zama tilas shugaban PDP ya cika alƙawarin da ya ɗauka na sauka idan ɗan takara ya fito daga Arewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya jaddada matsayarsa cewa wajibi shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi murabus duk da matakin da NEC ta ɗauka yau a Abuja.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa majalisar zartarwa mafi koli a jam'iyyar PDP (NEC) ta ƙaɗa kuri'ar amincewa da Dakta Ayu ya cigaba da jagoranci.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
2023: Dole Ayu Ya Yi Murabus, Gwamna Wike Ya Maida Martani Ga NEC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A 'yan kwanakin nan, Ayu ya kasance a kanun labarai kan saɓanin da ya shiga tsakaninsa da gwamna Wike, wanda ya samo asali tun bayan kammala zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Da yake martani kan matakin NEC, Gwamna Wike yace ba zai yuwu a yi watsi da yarjejeniyar da aka cimma ba, wacce Ayu ya ɗauki alkawarin sauka daga kujerarsa idan ɗan takarar shugaban kasa ya fito daga arewa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan ya bayyana cewa Atiku ya kai masa ziyara bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe tikitin PDP, inda ya nemi goyon bayansa tare da alƙawarin Ayu zai sauka daga muƙaminsa.

Wike ya nuna rashin jin daɗinsa bisa gazawar Atiku da Ayu wajen cika alƙawurran da suka ɗauka. ya jaddada cewa ba yadda za'ai ɗan takarar shugaban ƙasa da Ciyaman su fito daga yanki ɗaya ba tare da kulla wata manaƙisa ba.

Shugaban BoT ya yi murabus

Kwamitin amintattu (BoT) ya gudanar da taro yau a Abuja, inda shugaban kwamitin, Sanata Walid Jibrin, ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

A cewarsa, ya ɗauki wannan matakin ne domin kawo karshen rikicin PDP da kuma tabbatar da Atiku ya ɗare kujerar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa.

A wani labarin kuma Gwamna Aminu Tambuwal Ya yi murabus daga muƙamin shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya sauka da muƙamin shugaban kungiyar gwamnonin PDP.

Wannan matakin na zuwa ne biyo bayan murabus ɗin shugaban BoT, na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, wanda aka maye gurbinsa da Wabara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262