Machina Ya Magantu Kan Wasikar Dake Yawo Mai Cewa Ya Janyewa Ahmad Lawan Takarar Sanata
- Bashir Machina, 'dan takarar da ya lashe zaben fidda gwanin kujerar sanatan Yobe ta arewa a APC ya musanta janyewa daga takara tare da barin jam'iyyar
- A bayanin da ya fitar, ya jaddada cewa wannan wasikar bogi ce kuma an yi ta ne domin cimma wata manufa ta daban da bata masa suna
- 'Dan siyasan yace bai janyewa Lawan ba inda ya bukaci ofishin jam'iyyar na kasa da ya fitar da takardar karyata wasikar dake yawo, yace yana nan daram a APC
Yobe - Bashir Machina, 'dan takarar da yayi nasarar lashe zaben fidda gwani ta kujerar sanata mai wakiltar mazabar Yobe ta Arewa, ya musanta janyewa Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.
Wata wasika dake yawo a soshiyal midiya tayi ikirarin cewa Machina ya bar jam'iyyar APC kuma ya janye daga takara a zaben 2023 mai gabatowa, TheCable ta rahoto hakan.
"Wannan hukuncin na yanke shi ne saboda dalilin kaina dake da alaka da rashin jituwa tsakanina da shugabannin APC a jihar Yobe," wasikar tace inda aka aiketa ga shugaban jam'iyyar APC na kasa.
A yayin martani kan wannan cigaba, Machina yace ba gaskiya bane cewa ya janyewa Ahmad Lawan ko kuma ya bar jam'iyyar APC baki daya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Labari ya zo min na wasu marasa son zaman lafiya da suka yi wasikar bogi ta janyewata daga takara kuma suka bata min suna," NAN ta rahoto cewarsa.
"Kai tsaye nake bayyana cewa wannan wasikar ta bogi ce. Babu wani lokaci da na janye ko na bar jam'iyyar APC.
"Na sha mamaki da na gano cewa wasu mutane ne suka hada shirinsu na batar da jama'a ballantana magoya bayana zuwa yarda cewa na janye.
Ya yi kira ga sakateriyar jam'iyyar APc ta kasa da ta fitar da takarda kan batun wasikar bogin inda ya kara da cewa ya umarci lauyoyinsa da su shigar da karar duk wadanda ke da hannu a lamarin.
An samu wasu tarin hargitsi da hayaniya kan tikitin takarar kujerar sanatan Yobe na arewa.
A zaben fidda gwani da aka yi a watan Mayun da ta gabata, Machina yayi nasarar lashewa ba tare da abokin hamayya ba.
Amma an ce Lawan ya shiga takarar a wani zaben fidda gwani wanda APC ta shirya bayan da ya rasa tikitin takarar shugabancin kasa a watan Yuni.
Akwai labarai dake bayyana cewa, an bukaci Machina da ya janyewa Lawan, cike da hargitsi jam'iyyar APc ta mika sunan shugaban majalisar dattawan matsayin 'dan takara ga INEC.
Sai dai hukumar zaben mai zaman kanta ta shaida cewa APC bata da 'dan takara a yankin Yobe ta arewa.
Babu Tsuntsu, Babu Tarko: 'Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Ya Ki Janyewa Ahmad Lawan
A wani labari na daban, duka biyu kenan ga shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan. 'Dan takarar kujerar sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC kuma wanda ya ci zaben fidda gwani, Bashir Machina, ya ki janyewa Lawan.
Lawan, wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa a majalisar dattawa, ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu a zaben fidda gwani na neman tikitin takarar shugabancin kasa da aka yi a ranar 8 ga watan Yuni.
Da farko an fara bayyana shugaban majalisar dattawan a matsayin 'dan takarar yarjejeniya na jam'iyyar, amma gwamnoni 13 na arewacin Najeriya sun yi watsi da lamarin inda suka ce ya zama dole a mika mulki kudancin kasar nan.
Asali: Legit.ng