Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Da Fice APC, Ya Koma Jam'iyyar LP
- Fitaccen Jarumin fina-finai da ya watsar da APC saboda takara Musulmi da Musulmi ya koma jam'iyyar LP
- Kenneth Okonkwo, ya nuna jin daɗinsa ganin yadda aka girmama shi a LP yayin tabbatar da sauya shekarsa a hukumance a Abuja
- Takarar Tinubu da Shettima ta tayar da kura a tsakanin wasu 'ya'yan APC kasancewar su duk mabiya addinin musulunci
Abuja - Fitaccen Jarumin Fina-Fanai a Najeriya, Kenneth Okonkwo, wanda ya ja hankali lokacin da ya fice daga APC kan takara Musulmi da Musulmi, ya shiga jam'iyyar Labour Party (LP).
Ya sanar da matakin shiga LP a shafinsa na dandalin sada zumunta Instagram ranar Laraba yayin da ya saka Hotunansa da shugabannin jam'iyyar a Abuja.
Jarumin ya nuna tsantsar jin daɗinsa bisa yadda shugabannin LP reshen babban birnin tarayya suka tarbe shi zuwa jam'iyyar hannu bibbiyu.
Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023
Ya kuma sha alwashin ba da gudummuwarsa wajen ganin ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP, Peter Obi, ya yi ɗare-ɗare kan kujera lamba ɗaya a Najeriya a zaɓen 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Okonkwo ya ce:
"Girmama wa ne da Alfarma yadda aka karɓe ni zuwa jam'iyyar LP ranar 23 ga watan Agusta, 2022 a Supreme God House, Apo, Abuja, ta hannun baki ɗaya shugabannin jam'iyya na FCT karkashin shugaba, Peter Diugwu."
"Zuwan waɗannan jagororin wurin da na shiga jam'iyyar LP a matsayin mamba a hukumance ya haskaka taron.Wannan zai sa na ba da gudummwata wajen ɗora mai girma Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa a 2023."
"Ina miƙa godiya ta ga ƙungiyar jakadun Peter Obi (DAPO) wanda nike matsayin mai magana da yawunta, bisa taimaka wa har na zama mamban LP domin samar da shugabanci mai kyau a 2023."
Ɗan tsagin gwamna Wike ya fice daga PDP
A wani labarin kuma Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Darakta Janar na kungiyar masoyan gwamna Nyesom Wike ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Hakan ta faru ne yayin da wasu bayanai suka nuna Wike da wasu gwamnonin PDP sun sa labule da Bola Tinubu a Landan.
Asali: Legit.ng