2023: Kwanaki Bayan Gana Wa da Tinubu, Obasanjo Ya Yi Wa Wani Ɗan Takara Addu'a
- Wani ɗan takarar shugaban ƙasa ya kai ziyarar girmama wa ga tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta
- Farfesa Christopher Imumolen, ɗan takarar kujera lamba ɗaya karkashin Accord Party ya shiga jerin waɗan da suka gana da Obasanjo
- Yayin ziyarar, Farfesa Imumolen, ya baiwa 'Baba Iyabo' kamar yadda ake kiransa kyautar allon rubuta na girmama wa bisa rawar da ya taka
Ogun - Kwanaki ƙalilan bayan ya karbi bakuncin Bola Tinubu, tsohon shugaba, Olusegun Obasanjo, ya karɓi wani bakon a katafaren gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
A wata sanarwa da aka aike wa Legit.ng Hausa, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Accord Party, Farfesa Christopher Imumolen, ya kai wa Obasanjo ziyara ranar Talata, 23 ga watan Agusta, 2022.
Sabuwar Matsala a PDP, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice, Ya Koma Bayan Wanda Yake So Ya Gaji Buhari a 2023
A wani Hoto da Legit.ng Hausa ta gani, an hangi ɗan takarar ya duƙa kan guiwowinsa yayin da Obasanjo ke masa Addu'a da sa Albarka.
Tsohon shugaban ƙasan ya kasance na farko da Farfesa Imumolen, ɗan takara mafi karancin shekaru ya kai wa ziyarar girma a ƴan makonnin da suka gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Imumolen ya karrama Obasanjo da kyauta ta musamman
Yayin wannan ziyara, ɗan takarar ya karrama tsohon shugaban ƙasan ta hanyar ba shi kyautar Allon rubutu ɗauke da, "Aikin mazan jiya, ba zai taɓa bin ruwa ba."
Da yake jawabi game da ziyarar, Farfesa Imumolen ya ce:
"Kyautar girmama wa ba muka ba shi alama ce ta yabo bisa kyakkyawan shugabanci na sadaukarwa da suka yi a baya. Ina cigaba da ziyarar neman shawari ne domin sauya shugabancin Najeriya daga 2023."
Imumolen ya kuma bayyana muhimmancin ziyarar da kuma addu'ar dattawan ƙasa ke da shi a burin da yake fatan cika wa na siyasa.
Ya ce samun addu'a da shawari daga babban mutum kamar Obasanjo yana da daraja mai girma da ta zarce tunani domin yana da kwarewar da zasu taimaki masu niyyar ɗare wa madafun iko.
A wani labarin kuma Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Darakta Janar na kungiyar masoyan gwamna Nyesom Wike ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Hakan ta faru ne yayin da wasu bayanai suka nuna Wike da wasu gwamnonin PDP sun sa labule da Bola Tinubu a Landan.
Asali: Legit.ng