Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Ayyana Kujerun Yan Majalisu Biyu Da Babu Kowa

Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Ayyana Kujerun Yan Majalisu Biyu Da Babu Kowa

  • Duk da haramcin Kotu majalisar dokokin jihar Ondo ta ayyana kujerun mambobinta biyu a matsayin waɗan da babu kowa
  • Kakakin majalisar ya umarci ya miƙa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa takarda domin sanar da ita matakin
  • Tun lokacin da yan majalisun da abun ya shafa suka nuna adawa da shirin tsige tsohon mataimakin gwamna kujerun su suka fara tangal-tangal

Ondo - Majalisar dokokin jihar Ondo ta bayyana kujerun yan majlisu biyu, Favour Towomewo da Success Torhukerjijo, a matsayin waɗan da babu kowa bisa zargin cin amanar jam'iyya.

Prremium Times ta rahoto cewa Misis Tomomewo na wakilatar mazaɓar Ilaje ta II a majalisar yayin da Mista Torhukerjijo ke wakiltar mazabar Ese-Odoa Majalisar dokokin.

Majalisar dokokin jihar Ondo.
Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Ayyana Kujerun Yan Majalisu Biyu Da Babu Kowa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Matakin da zauren majalisar ya ɗauka ranar Talata ya saɓa wa hukuncin da Kotun Akure ta yanke a watan Agusta, 2020, wanda ya haramta wa yan majalisun dakatar da takwarorin nasu guda biyu.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Shugaban APC Na Ƙasa Ya Magantu Kan Shirin Majalisa Na Tsige Shugaba Buhari

Majalisar ta bi abin da ke ƙunshe a wasikun da aka turo daga gundumomin mambobin biyu ɗauke da adireshin shugabar jam'iyyar APC, kuma daga bisani aka aike wa majalisa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin majalisar, Bamidele Oleyelogun, wanda ya bayyana matakin a wata takarda da Sakataren zauren, Taye Benjamin, ya karanta, ya ce daga yanzu kujerun su sun zama babu kowa.

Kakakin ya kuma ba da umarnin cewa a miƙa wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC wannan takarda domin ta san matakin da ta ɗauka.

Meyasa haka ta faru da yan majalisun?

Mambobin da abun ya shafa na cikin tawagar yan majalisu bisa jagorancin tsohon mataimakin Kakaki, Iroju Ogundeji, waɗan da suka yaƙi yunkurin tsige tsohon mataimakin gwamna, Agboola Ajayi, bayan ya sauya sheƙa daga APC zuwa ZLP.

Punch ta ce Tun wannan lokacin shugabancin majalisar ya killace su wuri guda yayin da suka yi ta faɗi tashin kare martabar kujerun su kan tsanar da aka ɗora musu.

Kara karanta wannan

APC Ta Faɗi Sunan Wani Gwamnan PDP Dake da Hannu a Matsalar Tsaron Jiharsa, Ta Nemi a Kayar da Shi a 2023

A wani labarin kuma Atiku da Tinubu sun gamu da cikas, wasu jiga-jigan APC da PDP sun Sauya sheka zuwa AP

Ɗan takarar jam'iyyar Accord Party, Adebayo Adelabu ya samu ƙarin goyon baya na wasu manyan yan siyasa a Oyo.

Wasu jiga-jigan APC da PDP tare da dumbin magoya bayan su sun bi sawun Adelabu zuwa Accord don ganin ya zama gwamna a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262